Masana sun bayar da hanyoyin samun mafita kan yadda za a samu zaman lafiya a duniya.
Masana sun bayar da mafitar ne a wurin gangamin taron neman zaman lafiya, wanda ya gudana a Jihar Kano da kungiyar matasan masu gwagwarmayar kawo zaman lafiya suka shirya karkashin jagorancin, Kwamared Hussaini Yakubu Takai.
Ambasada Dakta Salihu Nura Adam, wanda aka fi sani da Salihannur, masanin magunduna ta hanyar amfani da tsire-tsire, ganyayyaki, ciyayi, sauyoyi, sassake da sauransu, yana daya daga cikin manyan baki masu jawabi. Ya ce zaman lafiya abu ne mai sauki domin ya fara ne daga kanka da gidanka da makwabtanka, unguwarka, karamar hukumarka, jiharka, kasarka dama duniya baki daya.
Ya ce kowa zai iya ba da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya a duniya ta hanyar tsoran Allah da aiki na sanin ya kamata, domin addini ya ce ka bi gaskiya ka kubuta.
Shi kuwa fitatcen malamin jami’i, Dakta Muhammad Bin Abdallah ya ce a kokarinsu na samar da zaman lafiyane ya sa suke taimaka wa matasa ta hanyar daukansu aiki da ba su tallafi na sana’o’i da kayan noma da samar da makarantu da sauransu a matsayin wata hanya da suke ganin ita ce mafita ta samar da zaman lafiya a duniya.
Mataimakin shugaban jami’ar Sa’adatu Rimi, Farfesa Yahaya Isah Bunkure ya ce sai da zaman lafiya ne ake samun ci gaba ta kowacce fuska, kamar na tattalin arziki, lafiya, noma kasuwanci da ilimi, don haka akwai bukatar kowa ya ba da gudunmawarsa domin samun zaman lafiyar duniya.
A karshe, Ambasada Badamasi Gidan Ruwa da Santalin Takai Sunusi Inuwa da Ambasada Sa’ad Ahmad, shugaban kamfanin ‘Telecommunication’ dukkaninsu sun bayyana cewa kokarinsu na samar da zaman lafiya ya sa kowannensu ya bayyana yadda suka bai wa daruruwan matasa aiki domin tabbatar da tsaro da samun zaman lafiya.
Source LEADERSHIPHAUSA