Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA)a ta bakin Shugaban ta, Buba Marwa ta kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 450 tare da damke masu safarar kwayoyi guda 23,907 a tsakanin watan Janairun 2021 zuwa watan Oktobar 2022.
Shugaban hukumar NDLEA, Marwa shi ya bayyana hakan a warin bikin karramawa na karshen shekara da bayar da lambar yabo da kara wa jami’ai girma, wanda ya gudana a harabar shalkwatar hukumar NDLEA da ke Abuja.
Ya kara da cewa a lokacin gudanar da wannan bincike, hukumarsa ta samu nasarar cafke masu safarar miyagun kwayoyi guda 23,907 ciki har da hodar Iblis 29.
“Mun kwace sama da tan miliyan 5,500 ko kilogiram miliyan 5.5 na miyagun kwayoyi wanda tsabar kudinsu ya sama da biliyan 450.
“A wannan lokacin dai, mun lalata konar wiwi da ta kai eka 772.5.
A wani labarin na daban Babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya bayyana cewa yana nan kan ra’ayinsa bai yarda malami ya shiga siyasa ba, amma yana so a bambanta abubuwa guda biyu.
“Bana sha’awar malami ya shiga siyasa daban, amma idan ya kasance wannan malamin yana da wasu ilimi na rayuwa wanda ya shahara a kai, idan har ya shiga siyasa to ko ya yi kuskure ba za a danganta wannan kuskuren da addini ba. Abin da ake nufi dai ilimi ne kadai abin da ake bukata.”
Farfesa Makari ya kara da cewa akwai hakkin shugaba a kan talakawa, haka kuma akwai hakkin talakawa a kan shugaba wanda suka hada da biyyaya da kuma adalci.
Ya ce wannan zabe da za a gudanar shaida ce da Allah zai taimaya a kai ranar Lahira.
Ya ce duk wanda ka zaba kar ka dauka abin wasa, kamar yadda ake raba wa mutane kudi ko omo domin su zabi mutum.
A cewarsa, wannan kudi ko omo da aka ba ka domin yin zabe, ka tabbatar da cewa shaida ce wanda Allah zai tambaye ka a ranar tashin kiya.
Farfasa Makari ya shawarci mutane su duba wadanda suka fi yi musu zaton alkairi kamar yin adalci, tausaya wa al’umma, to ka gina zabenka a kan wannan turbali na zaben shugaba.
Ya ce lallai mutane su duba wanda zai fi yi wa al’umma abubuwan da suka kamata a zaben shugaba domin su, sai ka yi kokarin gina zabenka a kan wannan ma’auni, amma duk lokacin da al’umma suka makantar da idanuwansu da hankulansu suka gina zabensu kan yadda mutane ke dibar miliyoyin kudade suna wazawa domin a zabesu har su hau wasu mukamai a kan su magance matsaloli, to lallai ba a shirya ganin lokacin magance matsalilin ba.