A jiya asabar ne gamayyar marubuta da mawaka masu rajin neman ‘yanci gami da adalchi suka ziyarci jagoran harkar musulunci a najeriya sheikh Ibrahim Yaqoob Alzakzaky a gidan sa dake babbar birnin tarayyar Abuja.
A yayin ziyarar mawaka da marubutan sun jaddada godiyar su ga kagoran bisa damar ziyarar da aka basu sa’annan kuma sun kara jaddada aniyar su ta kasancewa tare da jagoran a fafutikar sa da yake na ‘yanto al’ummar najeriya daga sabuwar mamayar Afirka wacce yanzu haka tare ruruwa a najeriya dama sauran kasashen afirka.
Mazaiyartan wadanda ke karkashin jagoranci Alhaji Mustafa Umar Baba gadon kaya sun bayyana cewa wannan ziyara itace irin ta kuma ta musamman ta suka kawowa malam zakzaky domin jajanta masa bisa waqi’ar data auku shekaru shidda da suka gabata da kuma abubuwan dan suka biyo bayan ta na kame kame da tsare tsare wanda gwamnatin najeriya karkashin jagirancin shugaba Muhammadu Buhari ta dingi nyi.
A nasa bangaren jagoran harkar musulunci a najeriya ya bayyana jin dadin sa dandane da wannan ziyara inda ya hori mawakan da marubutan da suyi amfanai da hazakar da Allah ta’ala ya hore musu domin hidimtawa addini da kuma tabbatar da cewa sun taimaki wadanda ake zalunta a cikin gida najeriya dama sauran sassan afirka.
Wannan zaiyara dai na cikin ziyarce ziyarcen da shehin malamin ke karba daga sassa daban daban na bangarorin al’umma tun bayan fitowar sa daga gidan yari bayan shafe kusan shekaru shidda gwamnatin najeriya na tsare dashi ba bisa ka’ida ba.
Bayan kammala ziyarar dai mawaka da marubutan tare da shehin malamin sun guidanar sallar gami da addu’o’in samun zaman lafiya a kasar mu najeriya sa’annan aka kammala kowa ya kama hanyar komawa gida.
Majiyar mu ta samu tattaunawa da daya daga cikin maziyartan inda ya bayyana cewa yaji dadin ziyarar kuma ya kara samu kwarin gwuiwa domin cigaba da hidimtawa addini da basirar da Allah ya hore masa.