Rundunar sojojin Nigeria masu kula da yankin jihar Barno sun tabbatar da wasu manyan kwamandojin Boko-Haram sun mika wuya.
A kwanan nan Rundunar sojin kasar nan na kirga nasara a yakin da take da masu da’awar Jihadi a yankin arewa maso gabas.
Sarakunan jihar Yobe sun tabbatarwa da rundunar sojin Nigeria hadin kansu wajen yakar ‘yan Boko-Haram, a jihohin su.
Wasu manyan kwamandojin Boko Haram hudu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a jihar Borno.
Wata majiya da jaridar Leadership ta samu tace ta ce su kwamandojin tsoffin kwamandojin Abubakar Shekau ne a sansanin Njimiya.
Amma sun ajiye makamansu suka koma kungiyar ISWAP a tafkin Chadi bayan farmakin da suka kai dajin Sambisa a watan Mayun 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar Shekau.
Sai dai daga baya manyan kwamandojin hudu sun rusa muba’ar tasu ga ISWAP, inda suka gudu zuwa Sambisa inda anan suke gudanar da aikinsu.
A jihar Barno Hoto: Leadership
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai’ (OPHK), Manjo-Janar Christopher Musa ya ce kawo yanzu kimanin ‘yan Boko Haram 83,000 ne suka mika wuya.
Yawancin wanda suka mika wuyar a halin yanzu na ci gaba da karbar gyaran hali a cibiyoyin gyaran hali daban-daban a jihar Borno.
Zagazola ta rawaito cewa kwamandojin hudu da suka mika wuya sun hada da Mala’ana (Khaid), mai lakabin Gwamna, Abu Dauda (Munzir), Modu Yalee, (Kwamanda) Bin Diska, (Nakif),.
Sannan Kwamandojin Sun mika makamansu a ranar 12 ga Disamba, 2022 ga sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) da ke sintiri a Gwoza LGA. Mayakan ISWAP Sun Kashe Sojoji A Barno.
A wani labarin kuma kuma gidan radion Faransa RFI ta rawaito cewa dakarun mayakan ISWAP sun kashe sojoji da fararen hula a jihar Barno.
Wani mummunan hari mayakan suka kai a cikin wani ayarin motoci a garin Malam Fatori dake karamar hukumar Abadam na jihar Barno, wanda harin yayi sanadiyar mutuwar sojoji tara.
A dai harin an tabbatar da mutuwar jami’an hukumar ‘yan sanda guda biyu, bayaga tarin kuma fararen hula da suma suka rasa ransu a dalilin harin.
Jami’an hukumar jin kai da bada tallafin gaggawa sunce harin ya jikkata tare da raunata wasu mutane da dama.