Hankalin jaruma Mansurah Isah ya matukar tashi bayan cin karo da tayi da bidiyon ‘yan ta’adda suna zane fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Ta yi kira ga ‘dan takarar shugabancin kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu, da ya ceto mutanen da ke hannun miyagun ita kuma zata masa kamfen.
Ta sha alwashin zabensa tare da iyalinta, jama’arta da kuma duk wanda gidauniyarta ta taba rayuwarsa, za ta masa kamfen da jininta.
Bayyanar bidiyon fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane ya tada hankulan ‘yan Najeriya.
A sabon bidiyon da suka saki, an ga yadda suke zane jama’ar da ke hannunsu da sanyin safiya inda fasinjojin ke ta kuka cike da ban tausayi.
Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd.
Ba a bar jaruman Kannywood a baya ba, jarumai irinsu Ali Nuhu da Mansurah Isah sun bayyana tashin hankalinsu.
Wallafar Mansurah Isah ta ja hankalin jama’a inda tayi kira ga ‘dan takara shugabancin kasa na jam’iyya APC, Bola Ahmed Tinubu da yayi wani abu, ita kuma zata masa kamfen.
“Zuwa ga Bola Ahmed Tinubu, Wallah wallahi idan ka taimaka mana aka sako fasinjojin jirgin kasa Abuja Kaduna wadanda aka sace, wallahi zan zabe ka, iyalaina zasu zabe ka, jama’a ta za su zabe ka a yankina, duk wani wanda gidauniya ta taba amfana zai zabe ka.
Zan yi maka kamfen da jinina. “Za ka iya, za ka iya bada kudin da suke bukata.
Ka yi amfani da kudin kamfen din ka ka fitar da su, mu kuma zamu yi maka kamfen kyauta,” wallafar ta tace.
A Sabon Bidiyo Yan Ta’adda Sun Saki Sabon Bidiyon Yadda Suka Azabatar da Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna.
A wani labari na daban, Ƙungiyar yan ta’adda waɗan da suka kai hari kan jirgin ƙasa da ke aiki tsakanin Abuja-Kaduna sun yi baranar tarwatsa Najeriya baki ɗaya.
A wani sabon Bidiyo da yan ta’adda suka sake, sun nuna yadda Fasinjojin jirgin kasa da ke tsare a hannun su ke rayuwa da yadda suke azabtar da su.
A bidiyon wanda jaridar Leadership ta rahoto, ɗaya daga cikin yan ta’adda ya ce wannan harin da suka kai har ya ta da hankalin kowa to bakomai bane a cikin hare-haren da suke shirin kai wa.
Source:hausalegitng