Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci nan da mako biyu zuwa uku a samar da maslaha kan rikice-rikicen manoma da makiyaya a fadin kasar nan.
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohi da su samar da filayen kiwo ga makiyaya a jihohinsu don warware matsalolin da suka addabi bangarorin biyu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Minna, babban birnin Jihar Neja, a yayin da yake kaddamar da shirin noman zamani domin samar da wadataccen abinci a Nijeriya.
Kazalika, ya bukaci gwamnoni da su hada karfi da karfe domin kawo karshen matsalar abinci.
Rikicin manoma da makiyaya ya dade a Nijeriya, lamarin da ya kai ga salwantar rayuka masu yawa da tarin dabobbi.
Har wa yau, matsalar ta wanj bangare na da alaka da samar da ‘yan fashin daji, wadanda suka rikide zuwa mahara masu satar mutane domin neman kudin fansa.
A gefe guda kuma matsalar ta zama silar hana manoma da dama yin noma a gonakinsu, lamarin da ke barazana da samar da abinci a kasar nan.
A wani labarin na daban shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa, shine da kansa ya shiga ya fita har sabon shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu ya samu wannan mukami.
Rarara ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida, inda ya kara da cewa, yayi matukwar farin ciki da Ali Nuhu ya samu wannan mukami.
Da yake amsa tambayoyin yan jarida akan ko gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu wadda yayi ikirarin kafawa ta biyashi aikin da yayi mata a lokacin yakin neman zabe ta hanyar nada amininsa kuma jarumi Ali Nuhu matsayin shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya?
DUBA NAN: Yiwuwar Sojin Nijar Su Saki Tsohon Shugaba Bazoum
Rarara ya amsa da cewa, “ko kusa wannan abu da aka yi wa Ali Nuhu ba shine zai nuna an biya ni aikin da na yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, duk da cewa naji dadi sosai akan wannan mukami da Ali Nuhu ya samu amma wannan bai zama dalilin da zai sa ace an biyani ba.”