Mali tana nuna murnarta na ficewar sojojin faransa.
Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan Alummar kasar Mali ne suka yi Gangami a babban birnin kasar Bamako domin nuna farincikinsu game da janyewar sojojin Faransa daga kasar , inda suka kona tutar kungiyar tarayyar Turai Masu zanga zangar suna dauke da kwalaye da aka rubuta kalaman dake nuna cewa sojojin faransa a matsayin masu goyon bayan yan ta’adda.
A ranar juma’a da ta gabata ne shugaban gwamnatin soji na kasar Mali ya bukaci kasar faransa da ta janye dukkan sojojinta daga kasar ba tare da bata lokaci ba. Bayan daya sanya alamar tambya kan shirye-shiryen da kasar ke yin a janye sojojinta daga kasar watannin da suka gabata
Ana sa bangaren shugaban kasar Faransa Emanual macron ya sanar da janye sojojinta daga kasar Mali bayan da kasar faransa ta yanke dangantakarta da gwamnatin sojin kasar, ita dai faransa ta aike da sojojinta a kasar mali ne a shekara ta 2013 domin yaki da masu Ikirarin JIhadi day a kwashe shekaru ana yi, yanzu haka dai faransa na da dakarun soji 4600 a yakin Sahel 2400 daga cikinsu suna kasar mali ne.