Batun Mallam Abdul-Jabbar yazo da sabon salon da ‘yan kwanakin nan, ba’asan irin malamin da aka yankewa irin wannan hukuncin ba.
Batun dai ya zama batun da ya karade kafafen sadarwa na zamani da gidajen jaridu da mujallu.
Jama’a zasu jira su ji martanin da gwamnati zata mayar ko kuma jawabin da zatai game da shari’ar tunda itace ta shigar da shi.
Daliban Abdul-Jabbar sunce akwai abubuwan da basu gamsu da su a cikin hukuncin da kotu ta yanke ba.
Rahotan BBC Hausa Wannan na zuwa ne bayan da hukuncin da mai shari’a na babbar kotun musulunci ya sameshi da laifin yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Kamar yadda wa’azinsa da shari’arsa ke cike da cece-cece kuce haka ma hukuncin kisan da aka yanke masa ta hanyar rataya yake tattare da wannan kace nacen.
Mutane da dama suna ganin hukuncin ya dace, kuma ya zama izina ga yan baya kan kar su aikata irin wannan abun.
Me Almajiransa Suke Cewa Dalibansa sun shedawa
BBC Hausa cewa wannan hukuncin da kotun ta yanke cike yake da kuskure da kuma tambayoyi.
Hukuncin kisa babban lamari ne da sai iya gwamna ko shugaban kasa kan iya zartar da shi.
Daliban da malamin nasu zasu iya daukaka kara tsawon kwana talatin daga lokacin da alkalin.
Mallam Abdul_jabbar nada laqabin sarkin gida yayin da kuma almajiransa suka nada masa sarkin yakin shehu Usmanu Dan Fodio.
Daliban na yawan yi masa kabbara da kirari lokacin da yake gabatar da karatuttukansa.
Kamar yadda suke fada “koma waye” ma;ana sun fi kowa ilimi ko juriya wajen karatu da biya da da’a inde a batun karatun malamin nasu ne.
Zai Iya Daukaka Kara Kotu Ta bashi damar daukaka kara zuwa kotun sama, ma’ana yanzu idan Abdul-jabbar ya bar wannan kotun zai koma kasan kwansitushin ne, wanda dashi za’a yanke masa hukuncin, ba kamar yadda nan akai amfani da littafan musulunci ba. Kuma yana da damar da zai iya hakura bai dauaka kara ba ya jira hukuncin da za’ai masa na kisan ta hanyar ratayar.
Gwamnatin Kano bata Ce Komai Kan Batun Ba Har yanzu babu wani jami’i a gwamnatance da yai magana ko ya tofa albarkacin bakinsa game da shari’ar da aka yankewa Abul-Jabbar.
Amma a iya cewa a wata shari’a makamanciyar wannan, an jiyo gwamnan kano na cewa muddin fayil din yanke hukuncin kisa ya biyo ta gabanshi kan wadda ya kawo Manzan Allah wargi, sai a sa hannu akansa.