‘Yan ta’adda sun kai mummunan farmakin yankin kudancin Kaduna inda suka halaka rayuka 28 a yankunan Malagum 1 da Sokwong.
Kamar yadda shugaban karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, Mathias Siman ya tabbatar, ya w ga tabbatar da kisan mutum bakwai a yankin Sokwong.
Sai dai Kakakin karamar hukumar, Atuk Stephen ya sanar da cewa mutum 22 aka halaka a Malagum kuma jami’an tsaro har yanzu basu kai musu dauki ba.
A daren Lahadi, ‘yan ta’adda sun halaka sama da mutum 28 a farmaki mabanbantam a yankunan Malagum 1 da Sokwong a masarautar Kagoro dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
‘Yan Ta’adda Sun Kai Sabon Farmaki, Sun Halaka Mutum 28 a Kudancin Kaduna.
Shugaban karamar hukumar, Honarabul Mathias Siman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya sanar da Punch a ranar Litinin cewa, ya tabbatar da kisan gillar da aka yi wa mutum bakwai a yankin Sokwong.
Farmakin na zuwa ne kasa da kwanaki biyar bayan wani harin da aka kai Malagum 1 inda aka halaka mutum uku.
Kamar yadda yace, dukkan gidajen dake yankin Sokwong an kone su inda ya kara da cewa har zuwa yanzu bai tabbatar da kisan Malagum ba.
Mathias yayi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu yayin da jami’an tsaro ke ta tururuwar zuwa bincike yankin.
A daya bangaren, mai magana da yawun karamar hukumar Kaura, Honarabul Atuk Stephen, yace sama da mutum 22 aka tabbatar da kisan su a Malagum 1 yayin da takwas suka rasa rayukansu a Sokwong.
Atuk ya kwatanta kisan da abun tsoro yayin da yake kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su hanzarta kawo karshen lamarin.
“Farmaki a yankunanmu ya dawo sabo kuma ba a ji ko ganin jami’an tsaro.”
Yace, Ba a samu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ba domin tsokaci yayin rubuta wannan rahoton.
Miyagun ‘yan bindiga sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Dansadau A wani labari na daban, ‘yan ta’adda dauke da makamai sun rufe babbar hanyar Gusau zuwa Dansadau dake jihar Zamfara.
An gano cewa ‘yan bindigan sun je sace matafiya ne dake Kaiwa da kawowa a babbar hanyar bayan halaka ‘yan bindiga 15 da ‘yan sa kai suka to a Maigoge.