A makarantu kamar dai yadda abin yake a wurare da dama, kasar nan na fuskantar matsalolin da suka shafi tabarbarewar tarbiyya, kamar sace-sace, magudin jarabawa, rashin mutunta malamai da hukumomin makaranta zinace-zinace da shaye-shayen miyagun kwayoyi, amma yayin da kasar take ci gaba da neman yadda za ta yi da irin wadanna halayen sai ga shi an fito ta bayan gida da wasu al’aumran da za su ci gaba da rusa mana tarbiyar ‘ya’yanmu.
In ba haka ba, ta yaya za mu bayyana daliliin sanya abubuwan batsa dana ‘yan luwadi a littatafan karatu na ‘yan makarantar Firamare da na sakandari?
A kwana-kwanan nan ne kungiyar dalibai musulmi ta kasa MSSN ta nuna damuwarta a kan yadda aka cusa abubuwan da suka shafi jima’i da sauran karatun da suka shafi basta a cikin littatafan karatu na ‘yan makarantar firamare da sakandire a kasar nan.
Ganin irin wannan katobarar, dole mutum ya yi tambayar menene ya hada darussan Lissafi, Turanci, da sauran durussa da irin hotunan batsa da aka yi amfanim da su a cikin littafan makarantun ‘yan sakandire da firamare a Nijreriya.
Wannan na nuna shiri ne na gurbata halayar yara ‘yan makaranta, to da wani dalili?.
A daya daga cikin littafan lissafi na ‘yan makarantar firamare an ba da misali da “kwaroron roba 20 + kwaroron roba 5 – kwaroron roba 2 =ya kama”.
Abin tashin hankalin shi ne irin wadannan littatafan da ake amfani da su suna koya wa yara ne yadda za su karfafa zubar da ciki, nadigo, luwadi, amfani da kwaroron roba da kuma hanyar da za su yi amfani da kwaroron roban wajen yin jima’i, wanda haka ke nuna kokari ne nasu na sa yara a hanyar fuskantar abin da ya shafi jima’i tun suna kanana yara.
Wannan abin tashin hankali ne, musamman ma ganin cikin darussan da ake koyarwa sun hada da daukar ciki a kananan shekaru, irin zubar da cikin da yara ‘yan mata za suyi cikin sauki, koya wa yara wasu kalmomi na batsa da hanyoyin da za su kaucewa daukar ciki ta hanyar amfani da magungunan hana daukar ciki da kuma yadda za su ji dadin jima’i ba tare da sun dauki ciki ba, abin mamaki wai dukkan wadannan an amince da sanya su a littafan makarantun firamari da sakandire.
Abin tashin hankalin a nan shi ne yadda ake bayyana wa dalla-dalla yadda ake yin jima’i a cikin littatafan ana karfafa wa yara bukatar su rika mu’amala da masu fama da cutar kanjamau ta hanyar sumbata, karfafa zubar da ciki da kuma karfafa wa yara yin jima’i mai tsafta ta hanyar amfani da kwaroron roba, wadannan na daga cikin abubuwwan da ke a cikin littatafan.
A ra’ayin wannan jaridar, samar da abubuwan batsa a littatafai daidai ya ke da samar da su a fayafauyan bidiyo, babu dalilin da za a samar da littatafan karatu ya zama kuma sanya abubuwan batsa don yin haka zai gurbata hankulan yaran ya kuma haifar da yara mara tarbiya a cikin al’umma.
Amma a nan tambayoyin da ke a bakin yawancin al’ummar Nijeriya shi ne wai suwa suka jagoranci sanya irin wanna abubuwan a cikin littatafan makarantar yaranmu?
A kwanakin baya ne shugaban hukumar makaratun firamare UBE, Farfesa Hamid Bobboi, ya nuna damuwarsa a akan yadda aka samu tabarbarewar tarbiya a makarantunmu, ya dora laifin a kan yadda al’amarin tarbiya ya tabarbare a cikin al’umma.
“Abin tashin hankalin shi ne yadda dukkan gurbataccen tarbiya da ake samu a cikin al’umma ana samunsa a makarantumu musaman makarantan firamare,” in ji Farfesa.
Shugaban na UBEC ya lura cewa, hukumar ta gudanar da bincike a kan tabarbarewar tarbiya a tsakanin makarantunmu, an yi kokarin gano dalili da sakamakon gurbacewar tarbiya a tsakanin makaratunmu.
A kan haka UBEC ta gano cewa akwai bukatar sake duba littatafan da ake amfain da su a makarantumu domin tsaftace su daga dukkan abubuwan batsa masu lalata tarbiyar yaranmu.
Wannan kuma na nuna bukatar cewa ya kamata a samu masu nunawa UBEC halin da ake ciki na rashin tarbbiya a makarantunmu, musamman bukatan a duba irin littattafan da ake amfani da su a makarantun wanda hastari ne ga tariyar yaranmu.
Kamar yawancin ‘yan Nijeriya amfani da abubuwan batsa a littattafai makarantun mu tamkar wata barazana ce ga tarbiyar yaranmu a cikin al’ummar da Musulmi da Kiristoci suka fi yawa wanda kuma a bayyana yake cewa, addininmu ya haramta wadanna abubuwan.
Tambaya a nan shi ne wai shin hukumomin kula da buga littatafan da ake amfani da su a makarantun basu duba tare da amcewa da wadannan littattafan kuwa?, babu makawa dole wadannan hukumomin su amsa tambayoyin iyaye musamman iyayen da yaransu suka tabu sakamakon wadannan littatafan.
Bayan haka a akwai bukatar dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu su gaggauta janye littattafan daga makarantu a daina amfani da su.