A kokarinta na tabbatar da samun sauyi mai kyau a ayyukan makarantar, sabuwar shugabar da aka nada ta Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya ta Kano, Hajiya Rakiya Mukhtar, ta kafa kwamitoci da za su binciki dukkan al’amuran makarantar da nufin samar da yanayi mai kyau da inganci ga dalibai.
Idan dai za a iya tunawa, ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, ta nada Hajiya Rakiya Mukhtar a matsayin A.g Shugaban makarantaar fasahar kiwon lafiya ta jihar a wasika mai lamba MOH/STAFF-S/T.II/I mai kwanan wata 9 ga Yuni, 2023 bayan sake fasalin shugaban cin makarantar.
Sakamakon kuka da bukatar da daliban suka gabatar kan zargin tabarbarewar harkokin makarantar yasa Hajiya Rakiya kafa kwamitocin da zasu sake nazari kan makarantar domin tsaftace tsarin tare da gyara zarge-zargen da ake yi wa shugabannin da suka gabata domin samun nasarar karbar ragamar aiki tare da ci gaba da gudanar da ayyukan makarantar cikin sauki.
Ta ci gaba da cewa, an kafa kwamitocin ne domin duba duk wasu matsalolin da daliban makarantar ke korafi akai, inda ta ce an yi hakan ne domin dawo da martabar makarantar da aka bata ba wai don bata suna ko farautar kowa ba.
A wani labarin na daban tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya faɗa wa sashen Hausa na BBC cewa, sata aka je yi gidansa bayan gwamnatin jihar ta ce ta ƙwato wasu motoci daga gidan nasa da gwamnan ya ƙi mayarwa gidan gwamnati.
A ranar Juma’a ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ta ce jami’an tsaro sun shiga gidajen Matawallae biyu, a Gusau da kuma Maradun, inda suka ƙwato motoci har 40.
“Dukkan ɗakunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana’arsa ce sayar da motoci.