Mai magana da yawun majalisar wakilan Najeriya, Benjamin Okezie kalu yace majalisar na kokarin halasta noma da safarar wiwi.
Kamar yadda ya bayyanawa manema labarai a garin Abuja, yace an shirya taron kwanaki 2 da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan hakan.
Kalu ya bayyana yadda Najeriya ta girgiza saboda dogaro da man fetur inda yace akwai dama masu yawa tattare da noma tare da safarar wiwi Majalisar wakilan Najeriya ta shirya tsaf domin halasta amfani da wiwi a kasar nan.
Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da yayi jawabi kan amfani da damammakin da za a samu daga tabar wiwi a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Kalu ya ce majalisar ta shirya tsaf domin shirya taron kwana biyu da masu ruwa da tsaki a kan amfanin wiwi, Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda yace, ranar taron ita ce 7 da 8 ga watan Yuli kuma za a samu masana kimiyya, ma’aikatan lafiya, masu hada magunguna, manoma, kamfanonin inshora da kuma kamfanoni masu zaman kansu da za a yi taron dasu.
Yayi bayanin cewa kasashe irinsu Afrika ta kudu da sauransu a yanzu suna morewa sakamakon noman wiwi da suke yi kuma suna fitar da ita kasashen ketare.
“An kwatanta Najeriya da kasa da ta dogara da mai ba wai kasa mai man fetur ba. A gaskiya dole ne mu kara samo hanyoyin kudin shiga tunda mun san dogaro da mai ba mai yuwuwa bane. “Annobar korona a duniya ta fallasa rashin kafuwar kasashen da suka dogara da mai.
Har a halin yanzu tattalin arzikin kasar nan na cigaba da farfadowa daga halin da muka shiga. “Noma shine tushen arzikin Najeriya kuma wiwi tana samar da arziki. Wiwin da muke magana ita ce wacce za a shuka mai yawa kuma a siyarwa kamfanoni domin sarrafawa,” yace.
Ya kara da bayanin cewa, “Idan ana so hakan ta faru babu wata damuwa, dole ne a yi taro da masu ruwa da tsaki domin fitar da tsarika, yanayin bada lasisi da kuma kula da masana’antar. “Ina fatan taron masu ruwa da tsakin da za a yi na kwanakin biyu zai zama mai amfani kuma za a cimma matsaya mai kyau wacce zata bada damar halasta noma da safarar wiwi.”
A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan yace a yayin da yake mulki ya sha alwashin ba zai taba amfani da matsayinsa ba wurin ladabtar da jama’a ba ko musguna musu.
Jonathan wanda ya shugabanci Najeriya daga 2010 zuwa 2015 ya kwatanta mulkin da ya samu a matsayin wata dama ta wucin-gadi da Ubangiji ya bashi, TheCable ta ruwaito.
Ya sanar da hakan ne yayin jawabi a bikin murnar cika shekaru 50 na Charles Osazuwa, shugaban cocin Rock of Ages Christian Assembly da aka yi a Benin, jihar Edo a ranar Lahadi.