Majalisar wakilai ta gargaɗi EFCC kan sayar wa masu laifi kadarori
Kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke kula da kadarorin da hukumomin gwamnatin ƙasar suka ƙwato daga hannun masu laifi ya gargaɗi hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC da kada ta sayar wa masu laifin kadarorin da a yanzu take gwanjonsu.
Shugaban kwamitin Adejoro Adeogun ya ce kwamitinsa ya gano cewa akwai yiyuwar waɗanda aka ƙwace wa kadarorin su biyo ta bayan fage domin sake mallakar kadarorin.
Mista Adeogun ya ce kwamitin nasa zai ci gaba da sanya ido domin sanin waɗanda ake sayar wa da kadarorin.
Cikin watan Disamban da ya gabata ne hukumar EFCC ta fara gwanjon ababen hawa 649 a jihohin ƙasar tara da birnin tarayya.
Sauran kadadrorin da hukumar ta bayyana yin gwanjon su sun haɗar da ƙananan jiragen ruwa 15, da wani babban jirgin ruwa na dakon kaya a jihohin Rivers da Delta da kuma Legas.
Haka kuma a watan na Disamba ne hukumar ta bayyana yin gwanjon manyan gidaje masu alfarma 144, tare da filaye da ta ce ta ƙwace daga hannun ‘yan siyasa, da masu riƙe da madafun iko, da kuma masu zamba ta intanet a sakamaon laifukan almundahana da zamba cikin aminci da aka same su da aikatawa.