Majalisar Dattawa ta amince da karamin kasafin kudi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike mata na Naira biliyan 819.5.
Majalisar ta amince da kasafin a ranar Laraba, bayan da ta yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan kasafin kudi wanda Sanata Barau I. Jibrin, ya jagoranta.
Sanata Barau ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen kammala wasu manyan ayyukan, ciki har da gyaran hanyoyi da madatsun ruwan da ambaliyar ruwa ta lalata.
Ya kara da cewa za a samu kudin ne daga basussuka na cikin gida da gwamnatin tarayya za ta ciyo.
A cikin wasikarsa ya aike wa majalisar dokoki, kasafin kudin, shugaba Buhari ya ce ”Kasar nan ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa a wannan shekarar, wadda ta haddasa lalacewar gonaki a yayin da ake dab da girbe amfanin gona.
“Hakan kuma ka iya kawo matsalar karancin abinci a kasar nan”.
Ambaliyar ruwa ta yi mummaan barna a wannan shekara, lamarin da ya tilasta manoma da dama asarar amfanin gona.
Sai dai an hasashen cewar ana iya samun karancin abinci sakamakon ambaliyar ruwan.
A wani labarin na daban fusatattun gwamnonin jam’iyyar PDP guda biyar (G-5) sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a birnin Landan na kasar Birtaniya.
An ce dan takarar na jam’iyyar APC ya nemi amincewar gwamnonin biyar din da su mara masa baya a yayin wani gangamin taro da aka gudanar a ranar Talata.
Gwamna Nyesom Wike (Rivers), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue) da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da wasu jiga-jigan siyasa daga Kudu sun sha alwashin ba za su goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ba, sabida kin amincewa da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus bayan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sai dai jam’iyyar PDP ta yi barazanar hukunta gwamnonin kan duk wani aiki da zai saba wa dokokin jam’iyyar, inda ta jaddada cewa tana da karfin ladabtar da duk wani gwamna da ya bijirewa dokar Jam’iyyar.