Majalisar Dokokin jihar Adamawa ta amince tare da tabbatar da nadin Mai Shari’a Hapsat Abdulrahaman a matsayin Alkalin Alkalan jihar.
Amincewa da mace ta farko a matsayin babbar Alkalin Alkalan (CJ) da wasu biyu ya biyo bayan la’akari kan wasikar bukatar tantance su da neman amincewa da su da gwamnan Jihar Ahmadu Fintiri ya aike Majalisar wanda Kakakin Majalisar Aminu Iya Abbas ya karanta a gaban kwaryar Majalisar ranar Talata.
Gwamna Fintiri ya yi rokon amincewa da su din ne bayan shawarar nadin nasu da hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) ta yi.
Bayan karanta wasikar, mataimakin Kakakin Majalisar, Pwamwakeno Mackondo, ya tashi tsaye ya gabatar da bukatar amincewa da nadin.
A yayin da ake muhawara kan hakan, mambobin da ke wakiltar mazabar Numan, Verre, Guyuk da Demsa sun jinjina wa gwamna Fintiri ne bisa aike da sunayen manyan shugabanni a bangaren shari’a din domin neman amincewa da su.
Bayan kammala amincewar Majalisar ne, Kakakin Majalisar da ya jagoranci zaman ya umarci akawun Majalisar da ya sanar da gwamnan matakin da kwaryar Majalisar ta cimma domin daukan matakin na gaba.
Sauran manya a bangaren Shari’a da aka amince da su din su ne Ibrahim Wakili Sudi a matsayin Grand Khadi na kotunan daukaka Kara ta Shari’a da kuma Audu James Balami a matsayin shugaban kotun daukaka kara ta kotun al’adu.
Idan za a tuna dai a watan Satumban 2022 ne gwamna Fintiri ya nada Hapsat Abdulrahaman a matsayin Mai rokon mukamin babbar Alkalin Alkalan jihar.