Majalisar Dokoki A Najeriya Ta Amince Da Kafa Hukumar Yaki da Yaduwar Makamai.
Rahotanni dake fitowa daga Najeriya sun bayyana cewa Majalisar Dattawa a Najeriya ta zartar da kudurin kafa hukumar kula da yaki da yaduwar kananan makamai a tsakanin alummar Najeriya
Majalisar ta amince da wannan kuduri ne biyo bayan nazarin da ta yi kan rahoton da kwamitin tsaro da leken asarin kasa suka gabatar masa, kudurin ya kunshi abubuwa 3, bayan kammala karatun kudurin a majalisar Dattawa daga bisani an mika su ga kwamitin tsaro na kasa domin ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa akansu.
Anasa bangaren shugaban kwamitin sanata Ibrahim gobir a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar yace kudurorin guda 3 na neman kafa wata hukuma da za ta doru akan yaki da yaduwar kananan makamai a najeriya ne,kuma kudirin ya bi sashe na 24 na dokar kungiayr ECOWAS ga wanda yake son mallakar makamai.
READ MORE : Kasar Oman Na Goyon Bayan Iran Kan Halattaccen Hakkinta Na Neman A Cire Mata TaKunkumi.
Daga karshe ya nuna cewa Kirkirar hukumar zai tamaka wajen rage yaduwar makamai tsakanin alumma, bisa la’akari da yanayin tabarbarewar tsaro da ake ciki a kasar.
READ MORE : Mabiya Malam Zakzaky Sun Sha Alwashin Juyin Juya Hali A Najeriya.