Majalisar dattawa ta kasa ta ta tafi hutun wata daya domin bai wa ‘yan majalisar damar yin yakin neman zabe a manyan zabubbukan Kasar da ke tafe.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Laraba.
Ya kara da cewa “Muna addu’ar Allah ya bai wa wadanda ke son sake dawowa majalisar dattawan nasara a zaben da ke tafe”.
Haka kuma shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da jami’an tsaro da su tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe da jama’a zasu aminta da shi domin gujewa tashin hankula.
A wani labarin na daban dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana matsalar karancin man fetur da kuma shirin sauya fasalin kudi da Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bullo da shi a matsayin wani shiri na kawo tsaiko ga zabe mai zuwa.
Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su bari karancin man fetur ya sanyaya musu guiwa kan gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Tinubu ya bayyana karara cewa karancin man fetur da ake fama da shi tamkar zagon kasa ne sannan ya danganta lamarin da cewar da gangan na haddasa shi.
Dan takarar na APC ya bayyana haka ne a Abeokuta, yayin yakin neman zabensa a Jihar Ogun.
Yayin zargin cewar an hada baki da yin barna wajen samar da wutar lantarki, inda ya danganta sauya fasalin kudade da aka yi a matsayin wani shiri na dagula wa mutane lissafi.
“Suna yin zagon kasa ga samar da mai. Ko man fetur ko babu za mu je mu kada kuri’a kuma za mu yi nasara. Wannan juyin juya hali ne mafi girma kuma idan na fada muku, kun san abin da nake nufi. Kun san ni ne zan sauya komai.
“Sun yi ta shirin haifar da matsalar mai, amma a manta da komai. Ni, Asiwaju zan magance matsalar samar da mai har abada.
“Ni dan gida ne, na zo nan, kuma ba zan ba ku kunya ba, za mu karbi mulki.
“Wannan juyin juya hali ne, wannan zabe juyin juya hali ne. Sun yin makirci, amma za su sha kasa. Sun ce farashin mai zai karu kuma zai kai Naira 200 kowace lita.Ba sa son a gudanar da wannan zabe, suna son a murde shi,” in ji Tinubu.
Da yake magana game da tsare-tsarensa ga matasan Nijeriya, Tinubu ya yi alkawarin bullo da shirin ba da lamuni ga dalibai, tare da samar da tsarin ilimi wanda zai magance matsalolin malamai da tabbatar da cewa dalibai sun kammala karatu a lokacin da ya dace.
“Ina ba ku tabbacin abu daya: zan bai wa dalibai lamuni. Babu wanda zai daina zuwa Jami’ar saboda kudin makaranta. Ina ba ku tabbacin cewa babu wanda zai sake maimaita shekaru ba tare da ya kammala karatunsa ba.”
Source:LegitHausa