Majalisar Dattawa ta amince Shugaba Bola Tinubu ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.
Hakan ya biyo bayan wasikar da shugaban kasa ya aikewa majalisar dattawa ta neman amincewa.
Sai dai wasikar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta yayin zaman majalisar ba ta bayyana sunayen mashawartan na musamman ba.
Nadin na zuwa ne mako guda da rantsar da shugaban kasar a ranar Litinin da ta gabata.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Tinubu ya kuma bayyana nadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, yayin da Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa aka nada shi mataimakin shugaban ma’aikatan.
A ganawar da ya yi da kungiyar gwamnonin APC, shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benuwe kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume, a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
A wani labarin na daban babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da hukomomin EFCC, ICPC da DSS, daga tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, har sai kotun ta yi nazari kan takardar koken da hukumomin suka shigar a gabanta.
Alkalin kotun mai Shari’a Donatus Okorowo, ya bayar da umarnin akan takardar korafin da aka gabatar wa da kotun a jiya Litinin.
“A bisa wannan koken, kotu ta dakatar da hukomomin EFCC, ICPC da DSS, daga tsare zababben sanata Yari, har sai kotun ta sake zama bayan ta yi nazari kan kararrakin da ake tuhumar Tsohon gwamna, Abdul’aziz Yari”
Okorowo ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga wannan watan.