Majalisar dattawa ta amince da ƙaramin kasafin kuɗi da Buhari ya aike mata
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ƙaramin kasafin kuɗi da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya aike mata na naira biliyan 819.5
Majalisar ta amince da kasafin ranar Laraba, bayan da ta yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan kasafin kuɗi wanda Sanata Barau Jibrin ya jagoranta.
Sanata Barau ya ce za a yi amfani da kuɗin ne wajen kammala wasu manyan ayyukan, ciki har da gyaran hanyoyi da madatsun ruwan da ambaliya ta lalata.
Ya ƙara da cewa za a samu kuɗin ne daga basussuka na cikin gida da gwamnatin tarayya za ta ciyo.
A cikin wasiƙarsa ta aike wa majalisar dokoki kasar kasafin kuɗin, shugaba Buhari ya ce ”ƙasar ta fuskanci mummunar ambaliya a wannan shekarar, wacce ta haddasa cinye gonaki a yayin da ake dab da girbe amfanin gona. Hakan kuma ka iya kawo matsalar karancin abinci a ƙasar”.
Read More :
Shahurn Soleimani An ba da shi a cikin zuciyar mutanen zamanin Musulunci.
Ukraine na buƙatar ƙarin Gas da makamai – Zelensky.
Dambarwar Qaseem Soleimani da rawar da ya taka a Iraqi.
Mazauna Amurka da Kanada na bikin Kirsimeti ba lantarki,cikin bala’in sanyi.