Majaliasar Dattawan Najeriya Zata Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun Abia Dangne Da ‘Yan Takarar Zabe.
Majalisar dattawan Najeriya ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotu ta gwamnatin tarayyar a jihar Abia ta yanke na bawa jami’an gwamnati wadanda suke son shiga harkokin siyasa, kan cewa ba sa bukatar ajiye ayukansu kamar yadda dokar hukumar zaben kasar ta 84(12) ta zayyana ba.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa sanata Senata George Thompson Sekibo mai wakilatar jihar Rivers ta gabas ne ya gabatar da bukatar inda ya sami goyon bayan wasu sanatoci 79.
Kafin haka dai wata babbar kotun gwamnatin tarayyar kasar a birnin Ummahia a jihar Abia ta yanke hukuncin cewa ‘yan siyasa wadanda suke rike da mukaman gwamnati zasu iya shiga harkokin siyasa ba tare da ajiye mukamansu ba.
Banda haka karamar majalisar dokokin kasar, wato majalisar wakilai ta bukaci a daukka kara kan bukatar shafe dokar zabe mai lamba 84(12) wacce ta haramtawa jami’an gwamnati shiga harkokin siyasa a lokacinda suke kan mukamansu.
Majiyar ta kara da cewa akwai rashin fahintar kalmin , ‘Polical appointment’ da kuma ‘civil Servan’ wanda alkalin kotun na Abiya ya yi wanda kuma ya kai shi ga yanke irin wannan hukuncin.