Dubun wasu jami’an CJTF 8 ya cika a Maiduguri bayan an kama su suna kai wa ‘yan Boko Haram bayanan sirri tare da samar musu da abubuwan bukatun yau da kullum.
An kama masu hada kai da ‘yan ta’addan karkashin jagorancin Mohammed Dungus a wurin rafin Yukami dake Banki inda suke kulla harka da ‘yan ta’addan.
Tuni dakarun sojin bataliya ta 151 suka bazama neman sauran masu leken asirin, kai bayanan sirri da miyagun lamurran ga ‘yan ta’addan a cikin garin na maiduguri.
Dakarun Bataliya ta 151 ta sojin kasan Najeriya a karkashin aikin rundunar Operation Hadin Kai a Banki dake jihar Borno ta damke matasa takwas ‘yan sa kai da ake zargi da taimakawa Boko Haram.
An gano cewa suna samar da kayayyakin bukatu da walwala ga kungiyar ta’addancin, Sahara Reporters suka rahoto.
Kafin kamen, wadanda ake zargi, suna aiki tukuru wurin kai wa ‘yan ta’addan bayanan sirri kuma suna da hannu wurin samar musu da miyagun kwayoyi, man fetur, gidan sauro, taliya da saura abubuwan da sukan bukata.
Bayanan sirri da aka samu daga jami’an tsaro, kuma jaridar Leadership ta samu yace, dubun wadanda ake zargin ya cika yayin da suke kulla wata harkalla da ‘yan ta’adda a rafin dake kauyen Yukami a wajen Banki dake karamar hukumar Bama.
Majiyoyi sun ce ana wannan miyagun al’amuran ne karkashin shugabancin wani Mohammed Dungus kuma hakan ya dinga zama hatsari ga dakarun sojin dake aiki a yankunan Banki.
Zagon kasa ga ayyukan sojojin da sharrin Dungus da mukarrabansa yasa ‘yan ta’addan ke kai farmaki kan dakarun da suka fita sintiri wurin kauyen Gauri a ranar 30 ga watan Oktoba.
Duk da cewa dakarun sojin sun dakile harin, an samu wadanda suka rasa rayukansu da kuma masu miyagun raunika a dukkan bangarorin.
Majiyar ta kara da cewa, ana cigaba da bincike don kakkabo sauran mazauna kauyen dake kai musu bayanai, leken asiri da sauran wadanda ke hada kai dasu.
Sai dai an tabbatar da cewa CJTF tuntuni ake amfani dasu wurin gano inda ‘yan ta’addan Boko Haram suke, dakile farmaki da kuma kwato garuruwa da kauyukan da Boko Haram suka kwace.
An kama dagacin kauye dake hada kai da ‘yan bindiga A kauyen Gobirau kuwa dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, jami’an ‘yan sanda sun yi ram da Malam Surajo wanda ke hada baki da ’yan bindiga wurin cutar da mazauna kauyen.
Source:Legithausa