An hallaka wani dan sanda wasu kuma sun samu raunuka a lolacin da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai harin a yankin Auno da ke a karamar hukumar Konduga cikin jihar Borno.
Auno na da tsawon kilo mita 24 da birnin Maiduguri cikin jihar Borno, ‘yan ta’addar sun kai harin ne a kan babbar hanyar Maiduguri zuwaDamaturu.
An ruwaito cewa, ‘yan ta’addar wadanda suka fito da yawansu, sun kai wa ‘yan sandan harin ne a yayin da suke kan yin aiki a wajen duba ababen hawa.
Wata majiya ta sheda wa Zagazola Makama, wani mai fashin baki kan harkokin tsaro a tekun Chadi cewa ‘yan sanda biyu da ke kan aiki a wajen duba ababen hawa ne suka aukawa ‘yan ta’addar da harbi, inda hakan ya janyo mutuwar ‘yan sandan.
Ya ce, jin harbe-harben ya sa sauran ‘yan sanda suka kawo dauki zuwa gurin suka kuma fafata Da ‘yan ta’addar , inda hakan ya sa ‘yan ta’addar suka ja da baya.
A wani lbarin na daban wata hazikar ‘yar Nijeriya mai suna Islamiyat Ojelade ta samu gurbin digirk na uku (PhD) a manyan jami’o’in Amurka guda 7 ba tare da yin digiri na farko ko na biyu ba.
Islamiyyat wacce ta sanar da nasararta a LinkedIn ta bayyana cewa ta samu damar samun gurbin karatu a jami’o’in da ke da digiri na uku. Ana ba da takardar shaidar HND a Nijeriya bayan kammala karatun shekaru 4 a manyan Kwalejin Ilimi.
Ta yi fice sosai daga makarantar inda ta samu maki 3.89, wanda hakan ya sa ta zama mafi hazakae daliban da suka kammala karatun 2018.
Islamiyat ta yi fafutukar wariya da ake wa masu takardar shaidar HND a Nijeriya.
Ta bayyana cewa bayan karatun digirinta na farko, ta rude kan matakin da za ta dauka na gaba. “Na tsorata kan abin da zan yi bayan karatun digirina. Na tattauna game da ‘babban burina’ tare da wasu mutane ciki har da abokai, iyaye da malamana,” kamar yadda ta wallafa a LinkedIn.
Ta lura cewa mutane kadan ne suka shiga don taimaka mata amma a karshe, ta samu tallafin karatu na PhD daga Jami’ar Jihar Florida, Jami’ar Massachusetts Amherst, Jami’ar Kansas, Jami’ar Kentucky, Jami’ar North Texas, Rensselaer Polytechnic. Cibiyar da Jami’ar Marquette a Wisconsin.
Dalibai da dama na samun guraben karatu a kasashen waje, musamman wadanda suke da hazaka sannan suka samu sakamakon jarabawa mai kyau
Source: Leadership