Kasuwannin man fetur da iskar gas na duniya na shirin sake fuskantar wani mako mai cike da kalubalen cinikayya bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare ta kasa a Gaza.
Tsoron hauhawar farashin danyen mai ya zama babbar barazana ga duk nahiyoyin duniya kasancewar yankin da ke samar da mafi yawancin man ne ke shirin afkawa yaki.
“Akwai damuwa ganin cewa, Gabas ta Tsakiya ke samar da kusan kashi uku na man fetur na duniya da Iran, wadda ke goyon bayan Hamas da sauran kungiyoyin rajin neman ‘yancin kai da ke yankin, Iran ta fada a karshen mako cewa, ‘kutsen na Isra’ila na iya tilasta kowa ya dauki mataki’.”
Gangar Danyen mai a kasuwar ranar Juma’a lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-hare ta kasa, farashin ya karu da kashi 3.2 bisa 100, inda farashin ya kai sama da dala 85 kan ganga guda.
Duk da cewa, har yanzun farashin bai ka kololuwar farashin da ya kai a kowanakin baya ba, inda ya kai sama da dala 90 kan kowace ganga amma dai akwai yiwuwar yakin ya yi tasiri a kasuwannin duniya.
Source LEADERSHIPHAUSA