Majiyar mu ta gano cewa mahara ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mata 7 a Sabon Kachiwe.
Wani jami’in Karamar Hukumar daga yankin da abin ya shafa wanda bukaci a sakaya sunansa ya shaida cewa mahara sun kuma kona kauyukan gaba dayansu, bayan sun yanka tare da harbe maza da mata.
Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya tabbatar da harin a kauyukan uku.
A wani labarin na daban kuma rundunar ‘yan sandan jihar Neja dake Najeriya ta tabbatar da sace Mahmud Aliyu, Hakimin Wawa a karamar hukumar Borgu ta jihar da ake zargin ‘Yan bindiga da aikatawa.
Jami’in yace, an yi garkuwa da hakimin ne a daren Asabar da misalin karfe 10 na dare a fadarsa, sai dai tuni ‘yan sanda sun fara bin sawun‘ yan bindigar don ceto hakimin.
A wani labarin daga jihar katsina kuma ‘Yan bindiga a jihar ta Katsina dake Najeriyar sun yi garkuwa da maidakin d’an majalisa mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin jihar, Ibrahim Aminu Kurami, da ‘ya’yansa guda biyu, bayan da suka mamaye Kuramin a daren Asabar.
Hakan na zuwa ne kusan shekara guda bayan sace dan majalisar da kansa.
Wata majiya tace, ‘Yan bindigar, da sukayi amfani da babura, sun tare hanyar Funtua zuwa Katsina na wasu lukuta yayin sace iyalan Kurami .