Wasu Mahara sun kai hari gidan Ardon Birni da kewayen Zariya da ke kauyen Daurayi ta jihar kaduna, Alhaji Shuaibu Mohammed inda suka halaka shi tare da ’ya’yansa Hudu a daren ranar Asabar din da ta gabata.
Matar marigayin, Mallama Halima Shu’aibu ce ta sanar da manema labarai cewa, Maharan su biyar ne dauke da muggan makamai suka afka musu gida da misalin karfe 10:00 na dare sannan suka fada dakin Ardo inda suka kashe shi nan take.
A cewar matar tasa daga nan nsai suka bi daki-daki na ’ya’yansa hudu, dukkansu magidanta, suka halaka su.
Matar ta bayyana sunayen ’ya’yansu da aka kashe a wannan harin da suka hada da Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da Haruna Ibrahim.
Halima ta kara da cewa bayan sun kashe su sai kuma suka kora shanunsu kimanin guda 100 a cikin daren.
Shi ma da yake magana da manema labarai, daya daga cikin ’ya’yan Ardon da ya rage, Abdurrahman Shuaibu ya ce bayan sun gama da gidansu, mahara har ila yau sun kuma harbi mutane biyu a kan hanyarsu ta barin kauyen.
Da manema labarai suka tuntubi mai magana da yawun Rundunar ’Yansandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce zai tuntubi babban jami’in ’yansanda na Zariya don jin cikakken bayanin yadda abin ya faru.
Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira don tabbatar da faruwar lamarin ba.
Ya zuwa yanzu jama’a nata jajanta wa kan lamarin.