‘Yan bindiga sun kutsa cikin wani masallaci sun kashe mutum 9 a garin Ba’are da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja.
An kashe masallatan ne a lokacin da su ke jam’in sallar Asubahin ranar Laraba.
Wannan mummunan kisa ya zo ne watanni biyu bayan da mahara su ka ritsa wasu masu jam’i a cikin masallacin garin Maza-Kula, su ka kashe mutum 17, su ka ji wa da dama raunuka.
Yayin da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Neja, Bala Karyas ya tabbatar da kisan mutum 9, wata majiya a garin da aka yi kisan ta shaida wa wakilin mu cewa mutum 12 ne aka kashe, kuma sauran waɗanda aka ji wa raununka duk an garzaya da su Babban Asibitin Kwantagora.
Makonni biyu da su ka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda ‘yan bindiga su ka raba mutane 151,380 daga gidajen su cikin shekara biyu, a Jihar Neja.
Gwamnatin Jihar Neja ta jaddada cewa a cikin shekaru biyu ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane su raba aƙalla 151, 380 daga gidajen su.
Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Ahmed Matane ne ya bayyana haka, inda ya ce akasarin waɗanda lamarin ya shafa duk manoma ne da ke cikin karkara.
Da ya ke bayani a ranar Lahadi yayin ganawar sa da manema labarai, Matane ya ce Hukumar Agajin Gaggawa ta Jiha ce ta tattara bayanan adadin alƙaluman.
Matane ya ce ya tabbata akwai ɗimbin masu gudun hijira da dama waɗanda ba a samu damar ƙididdigewa ba, saboda su na zaune tare da danganin su a cikin gidajen dangin.
Ya ce duk da cewa Jihar Neja na da sansanin gudun hijira biyu, amma waɗanda aka ƙididdige ɗin su na zaune ne a wasu sansanonin gudun hijira na wucin gadi, bayan an kai masu hare-haren.
Sakataren Gwamnatin ya ce an ƙididdige mutanen 151,380 daga ƙananan hukumomi 13, inda mutum 28,987 masu gudun hijira bayan raba su daga gida, duk ‘yan Ƙaramar Hukumar Rafi ne, wadda ta yi iyaka da Zamfara da kuma Kaduna.
An ƙididdige mutum 27,678 daga Ƙaramar Hukumar Shiroro, inda Boko Haram/ISWAP tuni suka fara yawon wa’azi a masallatan Juma’a, su na kiran jama’a su daina tura yara makarantun boko, kuma a bijire wa gwamnati.
Sai kuma mutum 11,678 a Paikoro, 22,754 daga Mariga, sai kuma mutum 8,913 da aka raba da muhallan su a Kontagora.
A Magama an samu mutum 998, mutum 8,907 a Mashegu, sai Wushishi mutum 2,010. A Rijau kuwa an raba mutane 5,809 daga gidajen su.
Ya ce gwamantin Neja ta Naira miliyan 300 kan mutanen da ‘yan bindiga su ka kora daga gida. Sannan kuma ɗaiɗaiku sun taimaka, sai Mai’aikatar Kula da Ayyukan Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa, ita ma ta kai na ta tallafi na miliyoyin nairori.
Cikin makon jiya ne wannan jarida ta buga labarin yadda Boko Haram sun kafa sansanoni a yankunan Shiroro da Borgu.
A karo na biyu Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansanoni a cikin Ƙananan Hukumomin Shiroro da kuma Borgu da ke cikin Jihar.
Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Jihar Neja ta ƙara fito da mummunan halin da ake ciki a yankunan, inda a cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Matane ya yi wa manema labarai ranar Talata a Minna, ya ce tuni har ‘yan ta’adda sun fara bi cikin Masallatan Juma’a su na wa’azi a ƙauyuka cewa jama’a su daina tura ‘ya’yan su makarantun boko, kuma a kowa ya tashi ya bijire wa gwamnati.
Matane ya ce a halin da ake ciki, ‘yan bindiga da ‘yan samame sun haɗe kai su na ƙoƙarin yaƙar gwamnati a Shiroro, su na bi masallatan yankunan su na kafirta gwamnati da kuma hana ‘ya’ya mata karatun boko.
“Garuruwan da ISWAP/Boko Haram su ka bi su na wa’azin sun haɗa da Shukuba, Koki, Kusare da Madaka.”
Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce ‘yan ISWAP ɗin har a cikin wa’azin su sukan ce, “Duk waɗanda su ka bi mu za mu kare lafiya da rayukan kowa. Amma abin da mu ke so shi ne ku bi mu a bijire wa gwamnati.”
Matane ya ce kuma su kan ce, “Gwamnati ta sani mu ba masu garkuwa da mutane ba ne. Allah ne ya aiko mu domin mu kafa ‘Daular Musulunci’.”
A cikin bayanin sa, Matane ya ƙara da cewa ISWAP na nan na ta ƙoƙarin kafa sansani a Gandun Dajin Babana da ke cikin Ƙaramar Hukumar Borgu.
Idan ba a manta ba, cikin 2020 sau da PREMIUM TIMES Hausa ta buga cikakken bincike na musamman, mai ɗauke da labarin cewa Boko Haram sun ɓulla a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Cikin watan baya rahotanni sun ce har yanzu gwamnatin tarayya bincike ta ke yi domin ƙoƙarin tabbatar da akwai su ɗin ko babu.