Hajiya Halima (Baba) Ibrahim, mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ta rasu tana da shekaru 86.
Mahaifiyar Sanata Lawan ta rasu a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, 2023, a gidanta da ke garin Gashua, karamar hukumar Bade a jihar Yobe.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa Sanata Lawan shawara kan harkokin yada labarai, Dakta Ezrel Tabiowo, ta ce za a yi jana’izar Hajiya Halima Ibrahim kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a ranar Lahadi 15 ga watan Oktoba, 2023, a garin Gashua da misalin karfe 11 na safe.
“Bayan haka, za a yi jana’izarta marigayiyar a babban masallacin Gashua, da ke fadar Sarkin.
“Sanata Ahmad Lawan ya yaba da irin yadda ake nuna soyayya da goyon baya kan rasuwar mahaifiyar sa.
“‘Yan uwa suna mika godiya ta musamman ga duk wadanda suka mika gaisuwar ta’aziyya da addu’o’i a wannan lokaci,” a cewar Dakta Tabiowo.
A wani labarin na daban al’ummar unguwar Kabong da ke Gada Biyu a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato sun wayi gari da wani mummunar ibtila’in annoba da sanyin safiyar ranar Asabar biyo bayan bindiga da Taransifoma ta yi cikin dare da ta yi ajalin rayukan mutum 7 hadi da jikkata wasu da dama.
Wakilinmu ya labarto cewa wutar da ta tashi ta samu asali ne daga jikin na’urar rarraba wutar lantarki (taransifoma), inda mummunar gobara ta barke da ta janyo firgici da razani ga al’ummar unguwar.
A cewar ganau, wanda ya nemi kada a bayyana sunansa a jarida, ya ce, mutum bakwai ne suka mutu, kuma gidaje da shaguna da dama hade da kadarorin miliyoyin naira ne suka salwanta sakamakon tashin gobarar da ta samo asali daga fashewar taransifomar.
“Abun bakin ciki da takaici, biyu daga cikin mutanen da suka mutu din ‘yan gida daya ne, wanda hakan ya janyo bakin ciki da bacin rai ga ‘yan uwansu,” ya kara da cewa.
Kazalika, kamfanin rarraba wutar lantarki ta Jos (JED) ta tofa albarkacin bakinta kan annobar, inda ta ce ta kadu sosai bisa lamarin da ya faru tsakar daren ranar Asabar wanda ya shafi kwastominsu da ke amfani da na’urar rarraba wutar lantarki ta Kabong Primary a unguwar Kabong da ke kan hanyar Rububa a Jos, babban birnin jihar Filato.
A sanarwar da shugaban sashin yada labarai na kamfanin, Dr. Friday Adakole Elijah, ya ce, binciken farko-farko da aka yi ya nuna cewa babban layin wuta mai dauke da balbalin wuta shi ne ya shiga layin karamin layukan wuta inda hakan ya janyo wutar ta tsallake iyakar da aka ware mata.
Ya ce, dukkanin matakan da ya dace su bi wajen tabbatar da gano hakikanin abun da ya janyo tashin wutar za su yi, kuma sun dauki matakan gaggawa na kare faruwar hakan a nan gaba.
Daga bisani kamfanin JED ya mika ta’aziyyarsa da jajantawarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda dukiyarsu ya salwanta.
Source LEADERSHIPHAUSA