Yayin da suka isa hedkwatar ‘yan sanda, mahaifiyar Hanifa Abubakar da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin diyarta Hakan ya faru ne a yau Juma’a yayin da aka kawo wadanda suka sace yarinyar suka hallaka ta a kwanakin baya.
Malamin Hanifa Abubakar ne ya sace ta, ya ajiye ta a gidansa na wani lokaci kafin daga bisani ya yi mata kisan gilla.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi rikici a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, yayin da Fatima Maina, mahaifiyar Haneefa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka ce malaminta ya kashe, ta hango mutumin da ya yi garkuwa da diyarta.
A baya an ruwaito yadda aka kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kawana, Kano, dangane da lamarin.
Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da Haneefa, kuma masu garkuwar suka bukaci a biya ta Naira miliyan 6 a matsayin fansa.
Yayin da yake kokarin karbar wani bangare na kudin fansan, jami’an tsaro sun cafke Tanko da wasu da ake zargi.
A ranar Juma’a, iyayen yarinyar da aka kashe da wadanda ake zargin sun hadu a hedikwatar ‘yan sandan Kano.
Iyayen yarinyar su ne suka fara isa wurin. Daga baya sai ‘yan sanda suka kawo Tanko da sauran wadanda ake zargin.
Nan take da Fatima ta hango Tanko, sai ta farmake shi, tana yi masa ruwan mari da kullin naushi a lokacin da take neman dalilin da ya sa ya kashe diyarta.
An ci gaba da rikicin na dan lokaci har sai da ‘yan sanda suka fatattaki suka shiga tsakani. Karin bayani na nan tafe..