Allah ya yi wa Mahaifiyar tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’abba, mai suna, Hajiya Rabi, rasuwa.
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP HAUSA cewa mahaifiyar tsohon kakakin Hajiya Rabi ta rasu ne a Kano a daren Alhamis bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Majiyar ta ce, za a yi sallar jana’izarta a ranar Juma’ar nan da misalin karfe 10:00 na safe a gidan Marigayi Alh. Bashir Tofa, da ke Unguwar Gandun Albasa, Kano.
Har ila yau, a cikin ‘Ya’yanta akwai Usaina Umar Na’abba, tsohuwar ma’aikaciyar gidan Rediyon Freedom da ke Kano.
A wani labarin na daban hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa, samar da cikakkiyen tsari na kiwon lafiya ga al’umma zai kai ga samar da al’umma masu koshin lafiya da za su iya bayar da gudmmawar su ga cigaba yankunan da suka samu kansu, a kan haka ne hukumar ta tsayu wajen gudanar da bukin ranar lafiya ta duniya da aka ware kowacce ranar 12 ga watan Disamba na kowacce shekara, wannan wata dama ce na jawo hankalin masu ruwa da tsaki a kan halin da harkar kiwon lafiya take ciki a sassan duniya.
Taken bikin wannan shekarar shi ne, “Samar Da Duniyar Da Muke Bukata: Samar Da Cikakkiyar Lafiya Ga Kowa Da Kowa.”
An karfafa bukatar samar da daidaito, aiki da gaskiya da kuma muhalli mai kyau tare da zuba jari mai inganci don samar da hukumomin lafiya ingantattu da za su iya tabbatar da ganin lafiyar al’ummar duniya tana gudana ba tare da wata matsala ba.
Shirin samar da lafiya ga al’ummar duniya zai tabbatar da gina cibiyoyin lafiya masu inganci a sassan duniya tare da bude kofar cibiyoyin ga kowa da kowa.
Samar da kiwon lafiya ga al’umma yana da nasaba ga ci gaba duniya gaba daya.
A irin wannan ranar ne ana kwatanta yadda cibiyoyin lafiya suke a sassan duniya da nufin irin bambancin da ake samu a tsakaninsu don hakan ya zama darasi mahukunta ta haka za su himmatu wajen an kara bayar da kokari don samun al’umma masu cikakkiyar lafiya a sassan duniya.
Saboda muhimmancin samar da cikakkiyar kiwon lafiya ga al’ummar duniya a halin yanzu an sanya lamarin a cikin muradun karni da ake fatan cimma a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2030, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi.
A kasashe da dama samar da cikakken tsarin kiwon lafiya yana neman ya fi karfin talakawa a cikin al’umma.
Babban ginshikin a tsarin samar da kiwon lafiya shi ne samar da ruwa a kan haka ne kungiyar ‘WaterAid’ ta bayar da rahoton cewa, harkar kiwon lafiya ta kasashe da dama ta rushe ne saboda yadda aka kasa samar da ingantaccen ruwan sha, haka ma an kasa samar da wutar lantarki ga al’umma yadda ya kamata.
Hakanan kuma Hukumar Lafiya ta Duniya da UNICEF sun bayar da rahoto a shekarar 2015 cewa, kashi 38 na asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da rahoton ya karkacde basu da hanyoyin samun cikakkken ruwan sha, kashi 35 kuma basu da ruwan da masu mu’amala da su za su samu isasshen ruwan da za su wanke hannu da shi don kariya daga cututtuka yadda ya kamata.
Rahoton ya kuma lura da cewa, in har jami’an kiwon lafiya basu iya tsaftace harabobin asibiti yadda yakamata to kokarinsu na bayar da cikakkiyar kulawa yana cikin gargara kenan.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa, tsarin nan na WASH wanda hukumar WHO da UNICEF ke daukar nauyi suna cikin tsarin nan na Majalisar Dinkin Duniya na ‘UN’s Global Action Plan” na tabbatar da ganin dukkan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin duniya suna samun isashen ruwa yadda yakamata don gudanar da ayyukansu nan da shekarar 2030.
Yana kuma da muhimmanci a lura cewa, samar da ingantaccen kiwon lafiya a duniya a bu ne daya shafi kowa da kowa, kuma a wannan lokacin ne ya fiye kowanne lokaci yakamata a tabbatar da dukkan cibiyoyin kiwon lafiyarmu sana samun kulawa yadda yakamata.
Cutar Korona da aka fuskanta a fadin duniya ta zama wani gwaji ga cibiyoyin kula da lafiyar mu. Hankalin shugabanin ya koma a kan bukatar tabbatar da ganin cibiyoyin kiwon lafiyan mu suna aiki yadda yakamata don fuskantar ire-iren wannan matsalar a nan gaba.
Haka kuma wasu na ganin shirin samar da kiwon lafiya kamar wani hakki ne da yakamata kowa ya samu amma wasu kuma na ganin lamarin a matsayin wata haja, saidai gaba daya lamarin samar da kiwon lafiya ga al’umma ya tashi daga wani abin da ba a dauka da muhimmanci ba zuwa wani abin da ya zama gaskiya musamman ma a kasashen duniya da suka cigaba.
Amma kuma ga wasu al’umma masu yawa, musamman na kasashe matalauta hakar sammar da kiwon lafiya harkan kamar a mafarki.
Rahoton hukumar WHO suka bayyana cewa, akalla rabin al’ummar duniya basu da zarafin samun cikakken kiwon lafiya kamar yadda shirin muradun karni SDGs ya tabbatar, da kuma kudurin majalisar dinkin duniya ya nema.
Wani lamari mai muhimmanci game da shirin samar da kiwon lafiya ga al’ummar duniya shi ne bukatar da ake yita sai mutane sun biya kudin kiwon lafiyar su wanda haka yana kara tura akalla mutum miliyan 100 ne zuwa cikin kangin talauci a duk shekara ciki kuma akwai ‘yan Afrika fiye da mutum miliyan 11.
Kashi 77.2 a cikin dari na ‘yan Nijeriya na cigaba da dogara ne da sayen magani a kemis a duk lokacin da suke fama da rashin lafiya.
Shirin samar da kiwon lafiya ga al’umma yana fuskantar matsaloli iri daya musamman a Nijeriya da sauran kasashen Afrika, cikin matsalolin akwai yadda aka fuskanci matsalolin da cutar korona ta haifar musamman daga hukumomi.
Amma kuma wasu mastalolin lamari ne da ta shafi duniya gaba daya, wadanda suka hada da yadda aka rika tattara bayanai, da zuba jari da batun samar da kwararru wadanda za su yi aikin da ya kamata na ganin an cimma burin da aka sa a gaba.
Haka kuma masana sun tabbatar da cewa, in har ana son cimma shirin samar da ingataccen tsarin kiwon lafiya ga al’ummar duniya dole ne a inganta asibitocinmu, a kuma horas da ma’aikatan lafiya da kara yawan cibiyoyin kiwon lafiyar a sassan Afrika.