Mabiya babban malamin na kuma shugaban mabiya mazhabara shi’a na afrika wanda ke zaune a najeriya Ayatullah Sayyid Ibrahim Yaqoob Alzakzaky sun shirya tsaf domin gudanar da tattakin arba’in na Imam Hussan (S) a ciki da wajen najeriya.
Kamar yadda wakilin mu ya rawaito mana mabiya malamin wanda bai jima da fitowa daga gidan kaso ba sun tabbatar da cewa bana ma kamar yadda suka saba zasu gudanar da wannan ibada mai dimbin falala kuma mai cike da tarihi.
Su dai mabiya malam zakzaky sun jima da fara gudanar da wannan tattaki inda a farko farkon sa sukan taka daga garuruwan su zuwa birnin zariya amma sakamakon canjin yanayi da aka samu suka koma zuwa babban birnin tarayyar abuja wanda a yanzun ma sun shirya hakan ne.
A kan samu mabiya daga cikin almajiran malam zakzaky din da sukan tafi kasar iraki a duk shekara domin yin musharaka a tattakin da ake gudanarwa daga birnin najaf zuwa karbala.
Labaran baya bayan nan sun tabbatar da cewa gwamnatin najeriya tana rike da fasfo din malamin da mai dakin sa wanda hakan ya hana su samun damar fita kasashen ketare domin ganin likitocin sun tun bayan shakar iskar ‘yanci da sukayi.
Idan lamurra sun tafi yadda ake tsammani ana sa ran ayi ma malamin da mai dakin sa sabbin fasfo domin fita kasashen ketare neman magani kamar yadda jaridar The Punch ta rawiato.
Bayan fitowar sa malamin ya gana da wasu daga cikin almajiran sa a gidan sa dake babban birnin tarayya abuja, sai kuma ganawar sa da ‘yan uwan sa na jini wanda ya biyo bayan hakan.
Labari na karshe da muka samu dangane da malamin shine hotunan sa da suka cika kafafen yada labarai yayin da yake zaune ana masa yankan farce duk dai a gidan nasa dake babban birnin tarayyar Abuja.
Sheikh Ibrahim Yaqoob Alzakzaky dai na zaman malami mafi tasiri a ciki mabiyan sa a fadin najeriya dama nahiyar Afirka baki daya.