Ma’aikatan hukumar aikewa da sakonni ta Nijeriya NIPOST, sun rufe babban ofishin hukumar da ke Abuja, suna zanga-zangar nuna adawa da nadin Tola Odeyemi a matsayin babban jami’in gudanarwa a hukumar.
Cif Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana a makon da ya gabata cewa, shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi wasu sauye-sauye a shugabancin hukumomin sadarwa da suka hada da NIPOST.
Sai dai jim kadan bayan da labarin nadin Odeyemi ya bulla, an samu rahotannin cewa an mayar da Adeyemi Adepoju, wanda aka kora daga mukamin babban jami’in gudanarwar humumar.
A cikin wani faifan bidiyo, an ga Adepoju yana jawabi ga wasu ma’aikata da suka yi ikirarin cewa Tinubu ya sake nada shi.
Sai dai a ranar Litinin ma’aikatan sun yi zanga-zangar sun kuma hana sabuwar shugabar hukumar ta NIPOST shiga ofishin hukumar, inda suka ce nadin nata ya saba wa muradinsu.
Ma’aikatan, wadanda suka ce sun fi son Adepoju, sun rera wakokin hadin kai da dauke da allunan nuna rashen amincewa da sabon nadin.
Source LEADERSHIPHAUSA