Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNMW), reshen jihar Kaduna, a hukumance ta janye yajin aikin da ta fara tun ranar 2 ga watan Oktoba. Dage yajin aikin ya biyo bayan nasarar da aka samu da jami’an gwamnatin jihar Kaduna.
Wata ganawa a ranar Alhamis, 24 ga watan Oktoba tare da mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jagoranci tattaunawa da shugabannin kungiyar da wasu manyan jami’an gwamnati wanda ya haifar da dakatar da yajin aikin.
Taron ya samu halartar sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma’aikata, da kwamishinan lafiya. An jaddada kudirin gwamnan na inganta jin dadin ma’aikatan lafiya da daukacin ma’aikatan jihar.
Duba nan:
- IMF ta musanta cewa tana bayan cire tallafin mai
- FEC ta amince da rancen dala miliyan 618 na jiragen yaki da harsasai
- Kaduna State nurses, midwives call off strike
A yayin taron an bayyana cewa gwamnan ya umurci kwamitin da ke kula da harkokin kwadago a karkashin jagorancin mataimakinsa da ya gaggauta tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadago a cikin kwanaki bakwai masu zuwa tare da mika rahoton aiwatar da su.
Za a yi la’akari da bukatun ma’aikatan kiwon lafiya a sabuwar tattaunawar mafi karancin albashi, tare da nuna himmar gwamnati don magance matsalolinsu da kuma tabbatar da ingantaccen yanayin aiki.
A wata takardar da ta raba wa mambobinta, kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa ta bukaci ma’aikatan jinya da ungozoma da su ci gaba da aikinsu daga karfe 12 na rana ranar Juma’a 25 ga Oktoba, 2024.
Sanarwar ta samu sa hannun jami’in hulda da jama’a kuma mukaddashin sakataren kungiyar, Conrade Yashi G. Nassa.
Dakatar da yajin aikin na nuni da wani gagarumin mataki na maido da zaman lafiya a bangaren kiwon lafiya na jihar Kaduna, domin a yanzu ana sa ran ma’aikatan lafiya za su koma bakin aikinsu, tare da samar da muhimman ayyuka ga al’umma.
Don haka kungiyar ta nuna jin dadin ta ga yadda gwamnati ke shirin shiga tattaunawa da kuma samar da hanyoyin da za su amfana da ma’aikata da ‘yan kasa da suke yi wa hidima.