Gwamnmatin tarayya ta hannun ma’aikatar bunkasa harkokin ma’adanai ta yi alkawarin aiki tare da manya-manyan kamfanonin harkokin ma’adanai na duniya don fitar da tsari na musamman da zai kai Nijeriya ga cin cikakkiyar gajiyar ma’adanai daban-daban da Allah ya shimfida a sassan kasar nan, wannan kuma zai zo ne a karkashin matakai 7 da gwamnati Shugaban kasa Bola Amed Tinubuy ya tsara.
Sanarwar haka ta fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga Ministan harkokin ma’adanai, Segun Tomori, ya kuma ce, wannan hadin gwiwar zai bunkasa sashin ta yadda zai kai ga samar wa Nijeriya kudin shiga mafi girma a cikin bangarorin tattalin arzikin kasar nan.
Da yake karbar bakuncin shugaban kamfanin ma’adanai na ‘PWC Partner’, Habeeb Jaiyeola, a ofishinsa, Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya yaba wa gudummawar kamfanin a nasarar da aka samu wajen gudanar da bikin makon ma’adanai da aka yi kwanakin baya.
Ya kuma gode wa shugabanin kamfanin a kan yadda ya jagoranci bangaren hakar ma’adanai a Nijeriya na tsawon shekaru, ya kuma yi alkwarin jawo su a jiki wajen kokarin samarwa da bangaren hakar ma’adanai alkibla na gari karkashin matakai 7 da Shugaba Bola Tinubu ya tsara.
Ya kuma ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana neman mayar da bangaren hakar ma’adanai kan gaba wajen samar wa Nijeriya kudin shiga.
A wani labarin na daban hukumar kula da albarkatun mai na cikin teku da tudu (NMDPRA) ta bayyana cewa, karancin kudaden waje da karyewar darajar Naira ya tilastawa kamfanonin kasuwancin man fetur dakatar da shigo da man fetur.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa, amfaniu da man fetur ya matukar raguwa, inda ya ragu da kashi 33.58, daga lita miliyan 66.7 a kullum kafin a janye tallafin man fetur zuwa lita miliyan 44.3 a kullum a halin yanzu.
Shugaban hukumar, Farouk Ahmed, ya bayyana haka a jawabinsa yayin taron masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur da aka yi a Legas ranar Litinin.
Ya kuma kara da cewa, kamfanonin safarar albarkatun man fetur 8 daga cikin kamfanoni 94 da aka bai wa lasisi suka samu nasarar shigo da jiragen ruwa 8 na man fetrur da ya kai 251,000 MT ( lita 291,238,670.69) a tsakaninwatan Yuni da Satumba na shekarar 2023.
Ya ce, raguwar da aka samu na kamnfanonin da ke shigo da man fetur wajen aikin shigo da man fetur ya faru ne saboda matsalar da kamfanonin suke fuskanta wajen samun kudaden kasashen waje na Dala.
Ya kuma nuna cewa, gwamnati na kokarin ganin ta hade yadda ake bayar da kudaden kasashenwaje ta yadda kamfanonin mai za su samu, ana kuma kokarin ganin an daidaita darajar naira a kasuwannin bayan fage.
“Ana fatan samar da man fetur zai kara tabbata tare da wadata in har matatar man Dangote ta fara aiki aka kuma yi wa matatatr man NNPC garanbawul suka fara aiki yadda ya kamata.
Ya kuma yaba wa kokarin gwamnatin Nijeriya na tabbatar ab samu wadatar man fetur a koda yaushe a fadin kasar a kuma farashin da ya dace.
Ya ce, cire hannun gwamnati gaba daya a bangaren zai taimaka wajen daidaita farashi da kuma karfafa al’ummar Nijeriya sun fara duba yiwuwar amfani da wasu makamashin da ba man fetur ba.
Source LEADERSHIPHAUSA