Likitocin Sudan sun kaddamar da zanga-zanga a yau Lahadi, don bayyana takaicinsu kan muna-nan hare-haren da jami’an tsaro ke kaiwa ma’aikatan kiwon lafiya, yayin zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke yi ta adawa da mulkin sojoji.
Zanga-zangar likitocin dai dai ita ce ta baya-bayan nan a Sudan, inda a makon jiya, a wata zanga-zangar ta daban, dubban mutane a arewacin kasar suka dates tituna, bayan da suka fusata da karin farashin wutar lantarki da aka sanar.
A ranar 25 ga watan Oktoban bara sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, suka yi wa gwamnatin rikon kwarya juyin mulki, lamarin da ya haifar da cikas ga yunkurin mika mulki ga farar hula zalla, tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019 bayan zanga-zangar da matasa suka yi.Matakin sojojin na Sudan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kasashen duniya tare da haifar da karin jerin zanga-zanga, inda ko a yau Litinin ake sa ran sake gudanar da wani gangamin Zuwa yanzu mutane 64 suka mutu yayi zanga-zangar adawa da mulkin sojojin a Sudan.