Gwamnatin Libya ta bude babbar hanyar da ta sada yankunan gabashi da kuma yammacin kasar da suka jima a rabe, sakamakon yakin basasar da ya biyo bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.
Fira Ministan Libiya Abdul Hamid Dbeibah ya jagoranci kawar da guma-guman duwatsu da kuma tarin kasar da aka yi amfani da su wajen raba yankunan na Yammaci da Gabashin Libya.
An dai shafe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin Sojojin Gwamnatin Libiya da mayakan Janar Khalifa Haftar da ke iko da yankin gabashin kasar, kafin daga bisani a cimma yarjejeniyar sulhun da ta kai ga kafa sabuwar gwamnati a karkashin Fira Ministan Abdul Hamid.
A wani labarin na daban jami’an tsaron Libiya sun ceto ‘yan ci rani 120 daga hannun kungiyoyi na masu safarar mutane da suka shafe lokaci mai tsawo suna tsare da su cikin azabtarwa.
Rundunar sojin Libiya ta ce mafi akasarin ‘yan ci ranin da ta ceto daga wani sansanonin gungun masu safarar mutane dake arewa maso yammacin garin Bani Walid ‘yan kasar Masar ne.
Garin Bani Walid mai nisan kilomita 170 daga kudu maso yammacin birnin Tripoli, yayi kaurin suna a kasar Libiya wajen zama cibiyar kungiyoyin masu safarar mutane gami da azabtar da su har ma kisan gilla a wasu lokutan.
Tun bayan barkewar rikici a 2011 bayan kashe tsohon shugaban Libiya Mu’ammar Ghaddafi da masu bore suka yi tare da goyon bayan rundunar sojojin NATO, kasar ta zama cibiyar da masu gudun hijira da ‘yan ci rani ke bi wajen tsallaka teku domin zuwa nahiyar Turai.
Rundunar NATO karkashin jagorancin amurka da sauran kasashen turai sunyi uwa sunyi makarbiya domin tabbatar da an kifar da gwamnatin muhammad gaddafi wanda hakan ya jawo rashin tsaro a kasar daya addabi kowa.