Kotu a Switzerland ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan wani tsohon kwamandan mayakan ‘yan tawaye a Liberia, bayan samunsa da laifukan aikata Fyade, kisan gilla, da cin naman mutane.
Karo na farko kenan da wata kotun farar hula ke yanke irin wannan hukuncin kan tsohon madugun ‘yan tawayen kungiyar ta Liberia ULIMO mai suna Alieu Kossiah da ya jagoranci tayar da kayar baya ga dakarun tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a shekarun 1990.
Kosiah da ya fuskanci tuhume-tuhume har 25 ciki har da cin zuciyar dan adam, ya shiga hannun jami’an tsaro a kasar Switzerland ne a shekarar 2014, kasar da yake zaune bayan samun takardar izinin zama ta dindindin.
A karkashin dokokin Switzerland da aka yiwa kwaskwarima a 2011, kotunan kasar na da hurumin hukunta manyan laifukan da aka aikata ko da kuwa ba cikin kasar ba ne ko nahiyar da take.
A wani labarin na daban cutar Ebola ta sake dawowa a kasar Liberia bayan mutuwar wata mata da ta harbu da annobar cutar a jiya alhamis kamar yadda hukumomin kiwon lafiya a kasar suka tabbatar.
A makonnin da suka gabata kasar Liberia kamar dai sauran kasashen yammacin Afkrka da suka yi fama da cutar sun bayyana kawo karshenta, abin da kuma hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar, sai dai kwanaki kadan bayan sanarwar, an sake samun wadanda suka kamu da annobar a Guinea da kuma wannan karo a Liberia.
An sake samun bullar cutar ne a Monrovia fadar gwamnatin kasar, kuma wata mata ce yar kimanin shekaru 30 a mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Yanzu haka hukumar lafiya ta duniya WHO sun tafi yankin da cutar ta sake bulla a Monrovia domin daukar mataki.
Ebola dai ta kashe Kimanin mutane 4,800 a Liberia kafin sanar da kawar da cutar a kasar a watan Disemba.