Gawar wani dan kasar Zambia, Lemekhani Nathan Nyirenda da ya mutu a filin daga garin kare kasar Ukraine ta iso Lusaka, babban birnin kasar ta Zambia.
An sauke gawar me a filin jirgin saman Kenneth Kaunada na kasa da kasa a ranar Lahadi, kamar yadda majiyar danginsa, Ian Nzaku Banda ta sanar a cikin wata sanarwa.
Ministan wajen Zambia ya bayyana cewa, gawar marigayin ta samu rakiyar jakadan Zambia na kasa Rasha, Mr Shadreck Luwita kuma ta samu tarbar sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mr. Chembo Mbula da danginsa.
Matashin mai shekaru 23 an ce yana karatu ne a kasar Rasha, kafin daga bisani gwamnatin kasar ta daure shi a magarkama bisa laifin ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
An ce an sake shi a watan Agusta bayan shafe shekaru biyu a magarkama.
Ya rasu a filin daga a watan Satumban bana
An sanar da ahalinsa da gwamnatin kasar kan rasuwarsa a watan Nuwamban bana kafin daga bisani a fara shirin dauko shi zuwa kasar, inda ya iso a jiya Lahadi.
A wani labari na daban: Daga 1876 zuwa bara
Tsakanin wadannan shekaru ne aka samu kirkire-kirkiren da suka sauya tsari da gudanuwar duniya zuwa yanayin da take a yau. Za mu dubi guda 10 daga cikinsu.
Bayan wannan sharhi, mai karatu zai fahimci lallai bunkasa da ci gaban duniya a fannin kimiyya da fasahar sadarwa ba abu ba ne na dare daya ba.
Ga 10 daga cikin wadannan manyan fasahohi da suka yi tasiri wajen sauya duniyarmu a yau:
Fasahar Tangaraho
Wannan fasaha ta samo asali ne a 1876, kuma wanda ya kirkiro ta shi ne shahararren masanin kimiyyar nan mai suna: Aledander Graham.
Ya samar da wannan fasaha ce sa’ar da duniyar Turai ke dogaro da fasahar Telegiram (Telegram).
Tun sannan ake ta inganta wannan fasaha ta tangaraho, har zuwa lokacin da tsarin bincike a fannin ya fara sauyawa, bayan game kasashen duniya da wannan na’ura ta wayar tarho.
Duk da cewa fasahar wayar salula na kan maye gurbin fasahar tarho, a tabbace yake cewa wannan fasahar ce asalin ci gaba a fannin sadarwa na zamani.
Fasahar Lantarki
A 1879, bayan kirkira da gwajin fasahar kwan lantarki, Thomas Edison ya nemi Hukumar Sadarwa ta kasar Amurka ta yi masa rajistar wannan fasaha don tabbatar da hakkin mallaka gare shi.
Bayan samun rajista, a 1880 aka fara amfani da kwan lantarki, wanda ke samuwa ta hanyar dumin makamashin lantarki. Wannan shi ake kira: “Incandescent Light.”
Daga nan kamfanonin samar da wutar lantarki suka ci gaba da samar da nau’o’i daban-daban na wannan fasaha.
Ya zuwa karshen bara, an kiyasta cewa akwai wutar lantarki na kan titi (Street lights) sama da miliyan 304 a duniya.
Sannan a kasar Amurka kadai ana da kwan lantarki masu rai guda biliyan 5.
A duk shekara ana sayar da kwan lantarki na zamani guda biliyan biyu da rabi.
A halin yanzu kusan kowace kasa da biranen duniya, wutar lantarki ta game ko’ina.