Kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta fusata bisa samun labarin yadda aka ci zarafin wata dalibar sakandare a jihar Legas
Shugabar makaranta a jihar Legas ta cire hijabin wata dalibar sakandare, lamarin da ya fusata kungiyar ta Muslunci.
Ana ci gaba da samun cece-kuce kan batun sanya hijabi a jihohin Kudancin Najeriya, lamarin da ke kara daukar zafi.
Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci ma’aikatar ilimi ta jihar Legas da ta binciki wata shugabar makarantar sakandaren Eletu Odibo da sauran malamai a makarantar bisa zargin cirewa wata daliba hijabi.
Shugaban kungiyar, farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba a cikin wata sanarwa da ya fitar, Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta bayyana, ana zargin shugabar makarantar, Mrs Christiana Sofuye da ba da umarnin a cire hijabin wata daliba mai suna Mujeebat AbdulQadri ‘yar aji biyu na karamar sakandare a bainar jama’a a makarantar.
An ci zarafin daliba, hakan ya saba dokar Legas da majalisar dinkin duniya.
MURIC ta ce, wannan aiki ya saba da doka kuma hakan zai iya tunzura al’umma matular ya ci gaba da faruwa.
Hakazalika, Akintola ya bayyana cewa, kotun koli a jihar Legas ta yi hukunci kan halascin sanya hibaji a makarantun jihar a ranar 17 ga watan Yulin 2022, kamar yadda kungiyar ta fada cikin wata sanarwa.
A bangare guda, ya ce cire ma dalibar hijabi daidai yake da cin zarafin yara da kuma take hakkin addini kamar yadda yanzo a bayanan majalisar dinikin duniya.
Hakazalika, ya ce ya yi mamakin yadda shugabar makarantar ta yi biris da umarnin gwamnatin jihar Legas na ranar 6 ga watan Disamba na ba dalibai mata damar sanya hijabi a makarantun gwamnati a jihar.
A jihar ta Kwara, an sha kai ruwa rana kan haramtawa dalibai mata musulmai sanya hijabi a makarantun gwamnati.
Hakan na ci gaba da daukar yanayi mara dadi a yankunan Kudancin kasar nan, gwamnati da hukumomi na daukar mataki.