Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama wani Igwedum Uche Benson, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja, a Jihar Legas dauke da kullin hodar iblis da ya boye a al’aurarsa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ta ce an kama Igwedum a filin jirgin sama na Legas a ranar Litinin 20 ga watan Yuni, lokacin da ya sauka daga jirgin Ethiopian Airlines wanda ya taso daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
Sanarwar ta ce, binciken farko da aka gudanar ya nuna wanda ake zargin, ya hadiye kulli 50 na hodar iblis kafin ya tashi daga kasar Brazil, sannan ya kasayar da kulli 48 a Addis Ababa, inda ya mika su ga wani mutum.
Sai dai ya yi ikirarin cewa ba zai iya fitar da sauran kulli biyu da suka rage ba, a lokacin da ya ke dakin otal da ke Addis Ababa ba kafin ya hau jirginsa, amma daga baya ya fitar da su a cikin bandakin jirgin a lokacin da ya tashi daga Habasha zuwa Legas.
Wannan ba shi ne karon farko da hukumar ke kama masu safarar miyagun kwayoyi ba, a ci gaba da yaki da ta ke yi na sha da kuma fataucin kwayoyin daga nan gida Nijeriya zuwa wasu kasashen.