Majalisar dokokin jihar Borno ta zabi Abdulkarim Lawan a matsayin shugaban majalisar ta 10.
Honarabul Lawan dai shi ne tsohon kakakin majalisa ta tara kuma ya kasance yana jagorantar majalisar tun a majalisa ta shida.
Magatakardar majalisar, Jidayi Mamza ya sanar da cewa majalisar ta samu sanarwa daga gwamnan jihar Babagana Zulum, na gudanar da zamanta na farko a ranar 13 ga watan Yuni.
“Majalissar ta samu sako daga mai girma gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, yana bukatar ta gudanar da zamanta na farko a ranar Talata 13 ga watan Yuni 2023 bisa la’akari da ikon da aka ba shi a sashe na 105 karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin 1999,” in ji shi.
Zababben dan majalisar mai wakiltar Marte, Gambomi Marte ya nemi takarar Abdulkarim Lawan sannan zababben dan majalisa mai wakiltar Jere, Abba Kyari Kolo ya mara masa baya.
Majalisar ta kuma zabi tsohon mataimakin kakakin majalisar Abdullahi Musa daga mazabar Askira Uba a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Dukkan mambobin biyu sun amince da nadin kuma sun bayyana shirin yin aiki.
A jawabinsa na karramawa jim kadan bayan rantsar da shi, Abdulkarim Lawan wanda ya shafe shekaru 12 yana shugabancin majalisar, ya yaba wa ‘yan majalisar bisa sake zabensa.
Ya kuma bukaci sabbin ‘yan kwamitin da aka kaddamar da su kara matsa kaimi tare da hada hannu da bangaren zartaswa domin kawo sauyi a jihar ta fuskar ilimi, samar da abinci, tsaro da dai sauransu.
Shugaban majalisar ya yi alkawarin aiwatar da manufar bude kofa don ciyar da majalisar zuwa wani mataki.