Wani mutun da ake kira Babatunde ya shiga hannu bayan da ya shafe shekaru goma yana bayyana kansa gaban kotun a matsayin lauyan da ya cika dukkan ka’idojin da ake cikawa domin zama lauya, alhali ba lauayan gaskiya bane.
Mutumin wanda aka kama shi a osogbo ta jihar osun ya shafe shekara goma yana ayyuka irin na lauyoyi, inda yake bayyana a gaban kotu domin gudanar harkokin shari’a kafin dubun sa ta cika.
Kamar yadda sakataren kungiyar lauyoyi na Osun ya tabbatar hukumar shari’a ta karbe tuhumar babatunde daga hannun ‘yan sanda bayan da kungiyar ta bukaci hakan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa dubun babatunde ta cika ranar 10 ga watan augudta inda ya bayyana kansa a gaban wata kotu domin gudanar da shsari’a amma yadda ya gabatar dav kana nasa ne ya saba da yadda lauyoyin gaske sukeyi wanda hakan ya fusata lauyan dayan banagren kuma ya sanya shakkun tabbatar babatunde a matsayin cikakke lauya a zukatan mahalarta kotun wanda da aka tsananta bincike sai aka gano babatunde dai lauyan boge ne kuma ya shafe shekaru 10 yana wannan harka, amma sai yanzu dubun sa ta cika.
Dama dai nan da can akan samu lauyoyin bogi wadanda basu karanta lauyanci a jami’a ba amma sukan bayyana kansu a matsayin lauyoyi wanda hakan ba karamin matsala bace wacce take addabar aikin lauyanci, kamar yadda wani lauya ya tabbatar mana.
A yanzu dai ana tsare da babatunde inda zai girbi abinda ya shuka domin ya zama izna ga sauran masu sha’awar aikata aiki irin nasa.
Sakataren kungiyar lauyoyi reshen jihar Osun dai ya tabbatarwa da wakilin mu cewa zasu tabbatar an dauki matakin daya dace kuma an hukunta babatunde domin toshe duk wata kafa ta samun ire iren a nan gaba.
Sai dai zuwa yanzu bamu iya jin ta bakin babatunde ba kamar yadda aka tabbatar mana yana hannun jami’an tsaro, kafin ya girbi abinda ya shuka.