Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.
Lamorde ya rasu yana da shekaru 61 a duniya.
Wata majiya daga iyalansa ta ce, Lamorde ya rasu ne a Masar (Egypt) a ranar Lahadi inda yake jinya
An haife shi a ranar 20 ga Disamba 1962, Lamorde ya kuma shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986 kuma ya yi ritaya a matsayin mataimakin babban sufeton ‘yansanda a shekarar 2021.
Lamorde ya rike mukamin shugaban hukumar EFCC tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
Lamorde shi ne Shugaban Hukumar na uku. An nada shi a matsayin shugaban hukumar a ranar 3 ga watan Nuwamba 2011 bayan da shugaba Goodluck Jonathan ya tsige Farida Waziri.
Majalisar dattijai ta tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar na uku a ranar 15 ga Fabrairu 2012.
Lamorde, an haife shi ne a ranar 20 ga Disamba 1962 a Mubi, Jihar Adamawa, ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin ilimin zamantakewa a shekarar 1984. Ya shiga aikin ‘yansandan Nijeriya a shekarar 1986.
A wani labarin na daban shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON, Malam Jalal Ahmed Arabi ya mika ta’aziyya ga ‘yanuwa da iyalan Marigayya Hajiya Tawakaltu Busare daga Jihar Kebbi, ta rasu ne a garin Makkah.
Wakilin Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON) a garin Makkah Dr Aliyu Tanko ya mika sakon a madaddin Shugaban.
A jawabinsa wajen ta’aziyyar, ya bayyana cewa, mutuwa na kan kowa a koyaushe kuma a ko ina. Daga nan ya umarci Ustaz Abubakar Lamin da ya yi addu’a ta musamman ga mamaciyar da fatan Allah Ya gafarta mata Ya Yi mata Rahama. Ya kuma sa muma mu cika da Imani idan tamu ta zo.
DUBA NAN: Kananan Hukumomin Kano Da Suke Cikin Barazanar Ambaliyar Ruwa
Ta bangaren Hukumar jin dadin Alhazan Jihar Kebbi kuma. Alhaji Garba Takware, ya nuna jin dadin yadda kan ace kwabo har Shugaban NAHCON ya aiko wakilinsa da jami’ansa domin taya su alhinin wannan rashin. Ya ce a wannan abin a yaba ne.