Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya koka kan yadda aka ware N345 miliyan matsayin kasafin ma’aikatarsa a shekarar 2023.
Mohammed yace bai ma san ta inda zai fara ba domin kan shi ya kulle, suna neman kudin bayyana nasarorin mulkin Buhari a yayin da wa’adin mulki yazo karshe.
Ya sanar da cewa dukkan hukumomin dake karkashin ma’aikatarsa an zabtare musu kasafin kudi inda yace idan ana don aiki, a karo musu kudi.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Juma’a ya koka kan N345 miliyan da aka yi kasafi domin manyan ayyuka a ma’aikatarsa a shekarar 2023 inda ya kwatanta hakan da abinda ba zai taba isarsu ba.
Lai Mohammed Ya Koka Kan N345m da Aka Warewa Ma’aikatarsa, Yace Kan Shi Ya Daure.
Yace ma’aikatar yada labarai tana bukatar isassun kudi domin bayyana nasarorin shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da wa’adin mulkinsa ke gangarewa, yaki da labaran bogi, kalaman kiyayya da sauransu wadanda ke barazana ga kasantuwar Najeriya kasa guda.
“Babu lokacin da yafi dacewa ma’aikatar yada labarai ta samu kudi kamar yanzu.
Ban san me zan yi da N345 miliyan ba. Ban san ta inda zan fara ba.
Ban san yadda zamu tsallake ba.
Idan kuna tsammanin da yawa daga gare mu, to ku bamu isassun kudi.”
Yace. Ya jajanta yadda manyan ayyukan ma’aikatarsa aka zabtare su daga N1 biliyan da aka bayar a 2022 zuwa N345 a 2023 wanda yace lokaci ne mafi muhimmanci ga ma’aikatar, Daily Trust ta rahoto.
Mohammed ya kara da jajanta cewa kudaden da hukumomin dake karkashin ma’aikatarsa suka yi kasafi duk an zabtare.
Shugaban kwamitin, Odebunmi Olusegun wanda ya koka kan karancin kasafin da aka yi wa ma’aikatar, ya kara da cewa ya dace a samarwa ma’aikatar kudin da take so don tayi abinda ya dace.
A wani labari na daban, ministan Watsa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, a ranar Talata, ya ce rashin isashen kudi da ake ware wa ma’aikatarsa duk shekara yana kawo cikas wurin yaki da labaran karya da maganganun kiyayya.
Mohammed ya bayyana hakan ne lokacin da ya gabata a gaban kwamitin majalisar tarayya ya sadarwa don kare kasafin ma’aikatansa na 2023, Daily Trust ta rahoto.
Source:legithausang