Muhammadu Buhari yana birnin Monrovia na Laberiya tun dazu da yamma inda ake bikin ‘yancin-kai.
Shugaban Najeriyan ya hadu da takwarorinsa irinsu Adama Barrowa da Umaro Sissoco Embalo Buhari ya bar kasarsa domin halartar wannan biki da kuma gabatar da jawabi a kasar Afrikar.
Muhammadu Buhari ya isa kasar Liberiya, inda zai halarci bikin taya kasar Afrikar murnar cika shekara 175 da samun ‘yancin-kai.
Hotunan isar Mai girma shugaban na Najeriya ya fito ne daga shafin Malam Buhari Sallau, daya daga cikin Hadiman Muhammadu Buhari.
An ga Buhari yana tare da mataimakin Shugaban kasar Liberiya, Jewel Taylor a birnin Monrovia a yammacin yau, 26 ga watan Yuli 2022. Kamar yadda hotunan suka nuna, a gefensu an ga Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, tare da Shugaban Laberiya, George Weah.
Haka zalika Muhammadu Buhari da sauran shugabannin kasashen sun hadu da Shugaban Gambiya, Adama Barrow a babban birnin kasar.
Sallau ya kuma wallafa hotunan Muhammadu Buhari wajen bikin taya kasar ta Liberiya murnar zagayowar ranar da ta samu ‘yanci a tarihi.
Buhari Sallau shi ne Mai taimakawa shugaban Najeriya a wajen harkar kafofin watsa labarai.
Buhari zai gabatar da jawabi Legit.ng Hausa ta na da labari cewa shugaba Buhari zai yi jawabi a kasar a game da abin da ya shafi sha’anin tsaro, harkar zabe da bin dokar kasa.
Fadar Shugaban kasa ta bakin Malam Garba Shehu ta bayyana wannan a cikin tasirin da za a gani na ziyarar da Buhari zai kai zuwa Monroviya. Liberiya ita ce kasar da ta fi kowace dadewa da samun ‘yanci a nahiyar Afrika.
A shekarar 1847 kasar ta bar karkashin mulkin mallakar Turawa.
Ana sa ran sauran manyan shugabannin kasashen nahiyar Afrika za su halarci biki da taron da za ayi a wannan kasa mai tsohon tarihi a Duniya.
Tir da wannan tafiya Dazu kun ji labari ana tsakiyar Allah-wadai da cin zarafin fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna da aka sace, sai ga shi Muhammadu Buhari zai yi tafiya.
Source:legithausang