Labari da dumi dumi da yake zuwa daga jihar kano yana tabbatar da cewa gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da harin ‘yan bindiga a hanyar sa ta zuwa zamfara.
Jihar zamfara dai ta shahara da yawaitar rashin tsaro, kama daga masu garkuwa da mutane zuwa masu satar shanu da dai sauran su.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa ba’a tabbatar da dallin harin ba amma dai an tabbatar da cewa an samu ceto rayuwar gwamna abdullahi umar ganduje daga hannun maharan.
Gwamnan jihar kano dakta Abdullahi Umar Ganduje na cikin gwamnonin arewa wadanda suka dage sosai domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar sa wanda hakan kuma ya zama babbar barazana ga masu neman tada kayar baya a yankin arewacin najeriya.
Cikakken labari dangane da wannan lamari na nan tafe…
A wani labarin na daban an bayyana kama shugaban ‘yan kungiyar biyafara a matsayin wani babban mataki na cimma nasara a kokarin samar da tsaro a najeriya amma anyi kira da a gaggauta sakin wannan shehin malamin shugaban darikar shi’a watau malam Ibrahim Zakzaky domin kotu ta jima da bada umarnina sake shi tare da mai dakin sa kuma a biyan sa diyya sakamakon bata masa lokaci da akayi na tsawon shekaru ba tare da yayi laifin komi ba.