Hukumar kwastom a Najeriya ta yi nasarar kame wasu kayayyaki masu ban mamaki da aka shigo dasu kasar.
An shigo da kakin soja da na ‘yan sanda Najeriya daidai lokacin da ake shirin yin babban zaben 2023.
An kuma kama wasu miyagun kwayoyi da aka shigo dasu daga kasashen Indiya da Pakistan kamar yadda aka bayyana.
Hukumar Kwastam a Najeriya ta yi nasarar kame wasu tufafin sojoji da na ‘yan sanda da aka shigo dasu kasar.
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, na kama kayan ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, kamar yadda BBC ta ruwaito.
A cewar rahoto, an yi fasa-kwabrin kayan ne daga kasar Afrika ta Kudu kuma sun shigo ne ba bisa ka’ida ba.
Bello Kaniyal Dangaladima ne ya bayyana hakan ga kafar labaran, inda ya bayyana dalla-dalla kayayyakin da aka kwato.
A cewarsa, daga kayayyakin da aka kwato sun hada da riguna, hulunan kwano na sojoji da kakin ‘yan sanda irin na Najeriya.
Baya ga kayan na jami’an tsaro, an kama wasu miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol na masu darajar Naira biliyan 37.
Ana kyautata zaton an shigo da miyagun kwayoyin ne daga kasar Pakistan da Indiya, kuma ana ci gaba da bincike a kai.
Wannan babban kamu dai nasara ce ga kwastom, kuma ya zo daidai lokacin da kasar nan ke shirin babban zaben 2023.