Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, Sun yi awon gaba da matashin Malami da ɗansa a jihar Kwara.
Bayanai daga mahaifin waɗanda aka sace, Imam Amolegbe, yace maharan sun nemi kuɗin fansa daga wurinsu.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar yace suna kan bincike kuma sun kama mutum 2 da ake zargi.
Miyagun ‘yan bindiga sun kai samame yankin Oko-Olowo, wata unguwa dake gefen Ilorin, babban birnin jihar Kwara da safiyar ranar Asabar, sun sace mutane uku.
Mutanen da harin ya shafa sun haɗa da wani matashin Malami, Alfa Sofiu Amolegbe, ɗan uwansa da ake kira, Fasansi da kuma ɗansa Aliyu.
Leadership ta tattaro cewa masu garkuwan sun farmaki mutanen ne a gidansu da ke Oko-Olowo, kan babban Titin Ilorin-Jebba kuma sun kutsa gidan ne ta taga.
Ɗan uwan Malamin, Fasansi ya yi yunkurin guduwa amma ‘yan bindigan suka harbe shi tare da daba masa adda sannan suka barshi jikin jini.
Mahaifin waɗanda aka sace, Imam Amolegbe of Dada, Limamin yankin Okelele, yace maharan sun bar Fasansi a zatonsu ya sheƙa barzahu amma a yanzu yana kwance a wani Asbitin kuɗi a Ilorin. Shin sun nemi kuɗin fansa?
Imam Amolegbe ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun tuntubi iyalai kuma sun nemi a haɗa musu miliyan N100m a matsayin kuɗin fansa.
Yace: “Masu garkuwan sun tuntuɓemu kuma sun nemi Miliyan N100m, mun rokesu su karɓi miliyan N10m duk da bamu da su.”
“Ina rokon gwamnatin Kwara da mutane masu fatan Alheri su taimaka mana mu kubutar da ‘ya’yana biyu da jikana daga hannun waɗannan miyagun.”
Legit.ng Hausa ta gano cewa tun bayan jin labarin mutane suka fara tururuwar zuwa jajantawa Uban waɗanda aka sace, wanda ya kasance babban Malami a Anguwar.
Wasu makusantan Shehin Malamin sun fara Addu’a domin Allah ya kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya.
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun ‘yan sandan Kwara, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da kai harin, yace tuni suka kama mutum 2 da ake zargi da hannu a garkuwa da ‘ya’yan malamin.
“Muna cigaba da bincike kan lamarin kuma muna gab da kubutar da su.
A halin yanzun mun kama mutum 2 da ake zargi,” inji shi. A wani labarin kuma tsagerun.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu miyagun sun halaka dakarun ‘yan sanda har uku a kan bakin aikinsu a jihar Enugu, kudu maso gabashin Najeriya.
Lamarin wanda ya auku a shingen binciken yan sanda dake Agbani ya tada hankulan mutane sakamakon yadda maharan suka buɗe wuta.
Source:Legithausa