An kama wasu ‘yan kasar waje mazauna Najeriya a kwara da suka mallaki katin zabe yayin da zabe ke karatowa.
An kwato katukan zabe 106 a jihar Kwara, hukumar shige da fice ta yi karin haske game da halin da ake ciki.
Saura kwanakin kadan a yi babban zaben 2023, an gargadi ‘yan kasar waje su guji yin zaben a Najeriya.
Hukumar kula shige da fice ta Najeriya (NIS) ta kama katukan zabe na PVC guda 106 a hannun wasu ‘yan kasar waje a jihar Kwara, TheCable ta ruwaito.
Aminu Shamsuddin, kwamtulan NIS a jihar ne ya bayyana hakan a ranar Litinin 6 Faburairu, 2023, inda yace an kama ‘yan kasar wajen ne a yayin sintirin da jami’an hukumar ke yi a birnin Ilorin na jihar.
A cewarsa, NIS ta yi shirin wayar da kan ‘yan kasar waje mazauna Najeriya game da ka’idoji da dokokin da ke tattare da zaben kasar, tare da ilmantar dasu matakin da ake dauka kan wanda ya saba.
Idan baku manta ba, kwanaki kadan ne ya rage a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, ana zaman dar-dar kan abin da zai iya biyo baya, rahoton Daily Post. Yadda ‘yan waje ke samun katin zaben Najeriya.
A cewarsa: “A lokacin wani shirin wayar da kan, ‘yan kasar waje sun tsorata da jin cewa duk wanda aka kama shi ya kusanci zaben Najeriya zai sha dauri, a maida shi kasarsu kana a sanya shi a bakin jadawali. “
Wasu daga cikin ‘yan kasar wajen da ke da katin zaben Najeriya da kansu suka ajiye katukan kuma suka koma kasashensu, za su dawo bayan kammala zaben.
“Yawancin mutanen da ke cikin wannan lamari matasa ne maza da mata, daga Jamhuriyar Nijar, Benin da Ghana. “
Sun ce wadanda suka basu wurin zama a Najeriya ne suka karfafa musu gwiwar yin PVC kuma wai su kada kuri’a a lokacin zabe don su kara adadin yawan kuri’u ga wasu ‘yan takarar da suke so.”
An kama wasu ‘yan kasar waje a Oyo A watan Nuwamban 2022 da ta gabata, mutum 18 ‘yan kasar waje aka kama bisa laifin mallakar katukan zaben PVC na Najeriya a jihar Oyo, Daily Post ta ruwaito.
Isah Dansuleiman, kwanturolan NIS a jihar ne ya bayyana hakan, inda yace an kama su ne a lokacin wani kame da jami’an hukumar suka yi.
Source:LegitHausa