Cibiyar Gudanar Da Harkokin Kasuwanci (ICA) ta karrama Kwanturolan Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS) a Jihar Ribas, James Sunday, bisa nuna kwazo, kwarewa da jajircewa wajen bayar da gagarumar gudunmawa a bangaren hidimta wa jama’a.
Wannan matakin na karamci da Mr James ya samu ya kai shi ga zama babban mambar cibiyar wacce aka lika masa alamin FCAI a cikin jerin sunansa.
A wata sanarwa dauke da sanya hannun Nwosu Chukwu, jami’in watsa labarai na NIS a jihar Ribas da ya fitar a ranar Asabar, ya kara da cewa an bada lambar yabon ne domin kara wa Kwanturolan azama a bangaren hidimta wa al’umma.
Shugaban reshen cibiyar ICA a jihar Ribas, Eze Sam Ubi Onyeka, wanda kuma shi ne daraktan gudanarwa a ma’aikatar yada labarai ta Fatakwal, ya mika wa James Sunday shaidar karramawar a wani kasaitaccen bikin da ya gudana.
Taron wanda ya samu halartar fitattun mutane da suka kunshi jami’an gudanarwa, daraktocin kamfanoni, jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi da suke jihar wadanda aka karrama bisa nuna godiya ga irin gudunmawar da suke bayarwa da kuma kamfanoni da suke gudanar da ayyuka na ci gaban al’umma da kuma sashin harkokin ilimi.
A wasikar da aka yi masa wacce ke alamta ba shi lambar yabon mai dauke da sanya hannun darakta kuma babban jami’in ilimi, Dakta Godswill C. Onyekwere, mai taken ‘Karramawa bisa gudunmawa ta kwarewa da gogewa a bangaren hidimta wa jama’a’.
“Wannan karamcin an ba ka ne domin nuna yabawa kan sadaukawa da kuma jajircewa wajen gudanar da aikin hidima wa jama’a tare da sanya kwarewa da kake yi wajen shawo kan lamura hadi da hangen nesa da kake da shi kan lamura.” In ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan matakin ya kai ka ga zama babban mambar cibiyar wanda aka lika maka shaidar FCAI a jikin sunanka. Muna taya ka murna da samun wannan babbar damar, muna maka fatan alkairi a tsawon shekarun da za ka shafe kana gudanar da aiki,” cibiyar ta sanar.
A jawabinsa na godiya, Kwanturola James Sunday, ya ce, wannan matakin lada ne ga irin aiki tukuru, sadaukar da kai, rashin son kai domin gudanar da aiki na kwarai, inda ya ce, “Wannan karamcin zai kara min kumaji wajen cigaba da yin aiki sosai domin al’umma.
“Abin a fayyace yake mutane suna nazarta kuma suna kallon ayyukan da muke gudanarwa, yana da kyau a kowani lokaci mutum ya zama mai yin aiki bisa cancanta.”
Ya misalta kyautar da ya samu a matsayin ni’ima daga Allah, sai ya sadaukar da ita ga jami’ansa, iyalansa bisa kwarin guiwar da suke ba shi a kowani lokaci da har ya iya cimma nasarori a rayuwarsa.
James ya karfafi sauran jami’ai da su kasance masu gudanar da ayyukansu bisa cancanta da nagarta hadi da gaskiya domin cigaban al’umma da kasa baki daya.
Source LEADERSHIPHAUSA