Kamar yadda akayi a shekarar 2015 da 2019, yan takarar kujerar shugaban kasa wanda suka hada da kwankwaso sun hadu da juna a Abuja.
Kwamitin Janar AbdusSalam Abubakar da Bishop Mathew Kukah sun shirya taron yarjrjrniyar zaman lafiya Wannan ne na farko da za’a yi sannan a sake yin wani yayinda zaben ya gabato a 2023.
Wasu yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da shugabannin jam’iyyunsu 18 sun hallara a farfajiyar ICC dake birnin tarayya Abuja da safiyar Alhamis, 29 ga Satumba, 2022.
Jiga-jigan siyasan sun hadu ne domin rattafa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya yayinda aka fara yakin neman zaben 2023.
Kwamitin Zaman Lafiya ta kasa NPC karkashin jagorancin tsohon shugaban kasan mulkin soja, Janar AbdulSalami Abubakar ne ta shirya zaman.
Yan takaran dake hallare a wajen sun hada Dan Takaran Shugaban Kasar AA, Manjo Hamza Al-Mustapha, Dan Takaran Jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, Dan Takaran Jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, Dan Takaran Jam’iyyar LP, Peter Obi, da sauran su.
An nemi dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, an rasa amma an ga abokin tafiyarsa, Kashim Shettima.
Tinubu, wanda a yanzu haka yana kasar Birtaniya, ba samu halartar taron saka hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya ba,wanda shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ke shugabanta.
Tinubu ya bar Najeriya a ranar Lahadin da ta wuce inda ya gana da wasu kungiyoyi a kasar Birtaniya. Sai dai akwai hasashe cewa ya je neman magani ne kasar.
Source:legithausang